✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aure dole

Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya shirya zai je su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a…

Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya shirya zai je su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ya isa gidan surukan nasa yana shan taba. Ga yadda hirarsu ta kwashe da mahafin yarinyar:
Saurayi: Baba ina kwana?
Baba: Lafiya lau, ashe da ma kana shan taba?
Saurayi: A’a, ba halina ba ne, na saba ne idan na sha giya ba na jin dadi, sai na sha taba.
Baba: Tabdi! Wato har giya ma kake sha ke nan?
Saurayi: A’a, idan na je gidan rawa ne kawai nake sha.
Baba: To, har gidan rawa kake zuwa?
Saurayi: Eh! Amma da can ba na zuwa, sai da na dawo daga gidan yari ne na fara zuwa.
Baba: Gidan yari fa ka ce, kai kuma me ya kai ka can?
Saurayi: kaddara ce ta sa na je, kisan kai na yi.
Baba: Kisan kai, wa ka kashe?
Saurayi: Wani baban budurwata na kashe saboda na tambayi auren ’yarsa ya hana ni.
Baba: Kai, Lale marhabin da saurayin ’yata. Gobe ka turo iyayenka mu yi maganar aure. (Mahaifin ya yi haka ne saboda tsoro, ya ji zancen kisa).
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382.