✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aure da zaman iyalin Kirista (8)

Aiki da hakki/nauyin maigida bisa matarsa da kuma zaman gida“Ku mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Kiristi kuma ya kaunaci ekklesiya, ya ba da kansa…

Aiki da hakki/nauyin maigida bisa matarsa da kuma zaman gida
“Ku mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Kiristi kuma ya kaunaci ekklesiya, ya ba da kansa dominta; domin shi tsarkake ta, bayan da ya tsabtata ta cikin wankin ruwa ta kalman, domin shi miko wa kansa ekklesiya, ekklesiya mai daraja, ba tare da aibi ko cira ko kowane abu misalin wadannan; amma ta zama mai tsarki marar aibi. Haka nan ya kamata mazaje kuma su yi kaunar matansu kamar jikunansu. Wanda yake kaunar matatasa kansa yake kauna: gama babu mutum wanda ya taba kin jiki nasa, amma yakan ciyar da shi yakan kiyaye shi, kamar yadda Kiristi kuma yakan yi da ekklesiya; domin mu gababuwa ne na jikinsa. Domin wannan mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa; su biyu kuma za su zama daya. Wannan asiri da girma yake: amma ina zance na wajen Kiristi da ekklesiya. Duk da haka sai ku kuma kowane dayanku ya yi kaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”(Afisawa 5:25–33).  “Ku mazaje, ku yi kaunar matanku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kolosiyawa 3:19). “ Haka nan kuma ku mazaje, ku zauna da matanku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin karfi, da kuma masu tarayyar gado na alherin rai: domin kada addu’oinku su hanu.” (1Bitrus 3:7).
A cikin makonnin da suka gabata, mun duba kadan daga cikin aiki ko nauyin mace a cikin zaman iyalin Kirista, amma kamar yadda muka sani, aure dai tsakanin mace da miji ne; kowa kuma yana da nasa hakki ga juna. Za mu so mu duba kadan daga cikin abin da ya kamata maigida ya yi. Allah Ya aminci cewa mutum zai iya ba da irin shugabancin da ya kamata musamman game da zaman gida, ya kuma nuna soyayya kamar yadda shi Ubangijinmu Yesu Kiristi zai yi; dole mutumin nan ya zama wanda ya gane kuma yana kishin ganin cewa matarsa ta girma cikin ban-gaskiya da kaunar Allah. Nauyin da ke kan maigida yana nan kamar yadda nauyin da ke kan Yesu Kiristi game da ekklesiya.

Mai gida ko miji shi ne kan mata:
“Gama miji kan mata yake kamar yadda Kiristi kuma kan ekklesiya ne, shi da kansa fa mai ceton jiki ne.” (Afisawa 5 : 23); “Amma ina so ku sani, kan kowane namiji Kiristi ne, kan mace kuma namiji ne; kan Kiristi kuma Allah ne.” (1Korinthiyawa 11:3); “ Ya sarayar da dukan abu kuma karkashin sawayensa, ya sanya shi kuma kai a bisa abu duka ga ekklesiya.” (Afisawa 1:22). Bisa ga tsarin Allah cikin halitta, lokacin da Ya yi mutum, Ya sa kan mutum a bisa gangan jikinsa, Allah ne Ya shirya haka, kodayake daga cikin kasusuwan hakarkarinsa ne Allah Ya dauki daya domin Ya halicci mace da shi; amma babu shakka cewa wurin da aka cire wannan kashi na hakarkarin yana kasa da kan mutum, idan za a gwada tsayin mutum, to lallai igiyar gwaji za ta soma ne daga kafa zuwa KAI. Kai shi ne wuri mafi tsawo a jikin mutum. Abu na biyu muhimmi kuma shi ne kowace gaba ta jikin mutum, tana da mahadi a KAI, kuma daga kai ne kowace gaba take karbar umarni ta wurin jijiyoyi (wadanda duka sun hadu a kai), ta yi ko mene ne ma. Kai ne yakan sa a gane mutum; misali idan an yanke kan mutum zai yi wuya a gane ko wane ne mai wannan gangar jikin, amma idan akwai kan a jiki, to babu wahala, za a iya gane ko wane ne, domin fuskar mutum a kai take. Abu na biye shi ne, idan mun lura – ido, kunne, hanci, da harshe; Allah cikin halittarSa Ya dasa su ne  a Kai. Kai din ne yakan yi mu’amala da sauran duniya duka, misali, Kai ne ke ba da umarni da baki, jiki kuma ya karba ta wurin kunne ko ido ko hanci, ko baki; jiki yana da hankalin ji da tabawa. Haka nan aiki ko nauyin da ke akwai tsakanin miji da matarsa. Idan kai na da irin wannan muhimmancin; dole ne mu lura da yadda za mu yi wannan shugabancin, idan kan mutum ya lalace, wahalar ba na kai kadai ba ne, duk jikin zai sha wahala. daya daga cikin aikin maigida shi ne; ya yi aiki kamar yadda Kai ke aiki ga jiki. Allah ne Ya tsara cewa miji shi ne kan mace, kamar yadda ya sa Kai bisa gangar jiki. Idan har miji da mata suna so su yi rayuwar da za ta gamshi Allah, dole su gane wannan tsarin da Allah Ya yi. Abin koyi a nan shi ne; miji ya kamata ya zama mutum natsattse, domin irin nauyin da ke kansa, dole ne ya kafu cikin ban-gaskiyarsa idan har zai yi shugabanci bisa ga maganar Allah. Maganar Allah na koya mana cewa maigida shi yake rikon shugabancin gida; kuma kowace mace idan tana so ta gamshi Allah cikin rayuwarta; ya zama dole ta kawo kanta karkashin shugabancin mijinta. Abin nufi shi ne, jagorancin iyali yana bisa mijin, ba wai an ce mace ba ta da ra’ayi ba a’a, amma idan ta kawo shawara, maigida ne ke da ikon yanke shawara bisa kowane abin da ya shafi iyalin. Abu guda da dole kowane magidanci ya lura da shi, shi ne; ikon da Allah Ya ba ka bisa matarka ba domin ka wulakanta ta ba ne, ko ka yi ‘mulkin danniya’ ko ka cuce ta ko ka ci zalinta ba ne, gama idan ka danne wa matarka hakkinta, to lallai sai ka san cewa kai ma, za ka gamu da Allah da Ya halicce mu duka; domin wannan duk lokacin da kake ba da umarni a gida, ka yi shi cikin tsoron Allah. Ka san cewa idan ba tare da jiki ba, babu yadda kai zai rayu shi kadai, ashe; idan babu matarka gaskiyar shi ne babu kai. Dole kowane magidanci ya bidi abin da zai fifita matarsa cikin Ruhu ta kuma kafu cikin ban-gaskiya idan yana son ta zame masa alheri, domin karuwarta da tagomashi na mijin ne. Maigidan zai zama sananne a kofar gari tsakanin dattawa; maganar Allah na koya mana cewa “Mijinta sananne ne a kofofin gari, Yayin da yana zaune a tsakiyar dattawan gari.” (Misalai 31: 23). Mene ne zai faru da jiki idan Kai ya lalace? Idan har miji bai iya ba da shugabanci mai kyau a cikin gidansa ba, to babu shakka wancan gida ba zai dade ba za a soma samun matsala daban-daban. Idan Kai ya lalace, ta gangan jiki ba zai zauna lafiya ba. Ka kula da jikinka.