✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aure da zaman iyalin Kirista (3)

DALILIN KO NIYYAR AURE. Ubangiji Allah ba ya yin kowane abu ba tare da dalili ba, komai wanda Allah ya halitta ko kwa ya yi,…

DALILIN KO NIYYAR AURE.

Ubangiji Allah ba ya yin kowane abu ba tare da dalili ba, komai wanda Allah ya halitta ko kwa ya yi, ya gama tunani a game da abin kafin ya yi shi. Allah bai yi aure domin jin dadin mutum ba ne kawai; babu yadda aurenka zai zama da kyau muddin ba ka san nufin Allah lokachin da ya kirkiro aure. Dole ne ka sani chewa akwai yadda Allah yake tunani lokachin da ya kafa tushen aure; kuma yana so ya ga dukan ma’aurata sun chika wannan nufin.  Duk lokachinda Allah ya dubi miji da matarsa, muradin zuchiyarsa shi ne ya ga chewa suna tafiya dai dai bisa ga tsarin da ya shirya tun daga farko. Shi ya sa kowane Iyalin Krista; dole ne su dukufa wurin yin addu’a domin su gane dalilin da ya sa Ubangiji Allah ya kawo su a matsayin miji da matarsa domin su iya chika wannan nufi. Masu Bi da dama ba su da lokachin addu’a su bidi nufin Ubangiji game da Iyalin su, wannan babban kuskure ne, domin idan ba mu roki Ubangiji Allah ya nu na ma mu nufin sa ba babu yadda zaman Iyalin zai gamshe shi. Bari mu yi dan binchike kadan game da dalilan da ya sa Allah ya kafa Aure tun daga farko; amma kafin lokachin, ina so in sake nanatawa chewa, auren da muke dubawa a yanzu, aure ne kamar yadda Allah ya tsara kafin mutum shi aikata zunubi. Ba irin auren da muka soma gani a chikin Litafin Farawa sura uku ba. Bayan zunubi ya shigo duniya, komai duka sai ya chanja mutum domin taurin kansa ne ya soma aure fiye da daya, har ya zama kamar babu damuwa ko kadan game da irin wannan hali.
Yesu Kristi ya yi magana a chikin Litafin Matta sura goma sha tara daga aya hudu zuwa takwas; “Ya amsa ya che, Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, na miji da tamata ya yi su, har ya che, Sabada wannan namiji za ya bar ubansa da uwarsa shi manne ma matatasa; su biyu kwa za su zama nama daya? ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama daya ne. Abin da Allah ya gama fa kada mutum shi raba. Suka che masa Don minene fa Musa ya hukumta a bada takarda ta kisan amre, a sake ta kuma? Ya che masu, Domin taurin zuchiyarku Musa ya bar ku ku saki matanku: amma BA HAKA YA KE DAGA FARKO BA.” Ashe akwai yadda Allah ya tsara Aure daga farko, amma domin rashin biyayyan mutum, sai mutum ya ratse ya bi nashi nufin. A chikin wannan koyaswan, ina so ne mu san minene ainihin tsarin da Allah ya yi game da aure; kuma mu ga yadda namu Iyalin zai gamshi Allah ta wurin chika nasa nufi. Bari mu dubi kima daga chikin dalilan da ya sa Allah ya kafa aure.
Aure Taimako ma mutum domin ya iya yin aikin da Allah ya ba shi: Lokachin da Allah ya halichi mutum, mun ga chewa akwai dalili, a chikin Litafin farawa sura biyu daga aya goma sha biyar zuwa ashirin, Maganar Allah na chewa “ Sai Allah ya dauki mutum, ya sanya shi chikin gonar Adnin domin shi aikache ta, shi tsare ta kuma. Ubangiji Allah kuma ya dokachi mutumen, yana chewa, An yarda maka ka chi daga kowane itachen gona a sake: amma daga itache na sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ka chi ba: chikin rana da ka chi, mutuwa za ka yi lallai. Ubangiji Allah kuma ya che, ba ya yi kyau ba mutum shi kasanche shi daya; sai in yi masa mataimaki mai dachewa da shi. Daga chikin kasa kuma Ubangiji Allah ya sifanta kowane dabba na jeji, da kowane tsuntsu na sama; ya kawo su wurin mutumen ya ga abin da za ya che da su: iyakar abin da mutumen ya kira rayayyen halitta, shi ne ya zama sunansa. Mutumen kwa ya bada sunaye ga dukan bisashe, da tsuntsayen sama, da kowane dabba na jeji; amma ba a samo ma mutum mataimaki mai dachewa da shi ba.”  Hakanan a chikin Farawa 1 : 27 – 28, maganar Allah na koya mana chewa “Allah ya halitta mutum chikin suratasa, a chikin surar Allah ya haliche ; na miji da ta mata ya haliche su, Allah ya albarkache su kuma: Allah ya che masu, Ku yalwata da yaya, ku ribu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a kasa.”