✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Augustine Eguavoen ya ajiye aikin horas da Super Eagles

Augustine Eguavoen ya ajiye aikin ne bayan cire Super Eagles daga gasar kofin nahiyar Afrika.

Kocin tawagar ’yan wasan Najeriya ta Super Eagles, Augustine Eguavoen, ya sanar da ajiye aikinsa bayan kasar Tunisiya ta yi waje da tawagarsa daga gasar cin kofin nahiyar Afrika a ranar Lahadi.

Eguavoen ya sanar da ajiye aikin nasa ne a taron manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce zai koma mukaminsa na asali na kula da harkokin wasanni na NFF.

Ya ce, “Dama na karbi kocin na Super Eagles ne na wucin gadi zuwa kammala gasar kofin nahiyar Afrika, tunda mun dawo gida zan koma mukamina na asali.

“Mukamina shi ne kula da harkokin wasanni a NFF, zan sauka na ba sabon koci damar gudanar da aikinsa,” cewar Eguavoen.

NFF ta ba wa Augustine Eguavoen jan ragamar tawagar Super Eagles na wucin gadi bayan sallamar Gernot Rohr, wanda ya shafe shekara biyar a matsayin kocinta.

A watan Disambar 2021 ne Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta nada Jose Peseiro dan asalin kasar Portugal a matsayin sabon kocin da zai ci gaba da jan ragamar tawagar ta Super Eagles.