✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Attajiran Rasha sun yi asarar Dala 39bn a rana daya

Asarar ita ce ta biyar mafi muni a tarihin kasuwar hannun jarin kasar Rasha, wato MOREX

Manyan attajiran kasar Rasha sun tafka asarar da kimarta ta kai Dala biliyan 39 a cikin sa’a 24 bayan kasarsu ta far wa Ukraine da yaki.

Attajiran na na Rasha sun shiga wannan tsaka-mai-wuya ne rana guda bayan takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa kasarsu bayan Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojin kasar su auka wa makwabciyarta, Ukraine.

Kafar yada labarai ta Bloomberg ta ce asarar da manyan masu kudin na Rasha da kamfanonin suka tafka ta shafi bangarori daban-daban a kasuwar hannun jarin kasar (MOREX), inda ta yi asarar kashi 33 cikin 100 a rana guda.

Rikitowar ita ce ta biyar a jerin manyan asarar da kasuwar hannun jari ta MOREX ta yi a ranar guda a tarihi; Wadda ta fi muni ita ce ta Dala bilyan 50 da ksauwar ta yi asara a ranar ‘Black Monday’ a shekarar 1987.

Manyan wadanda suka yi asara

Bloomberg ta bayyana cewa wanda ya fi tafka asara shi ne Shugaban Kamfanin Mai na Lukoil, wato Vagit Alekperov, wanda ya yi asarar Dala bililyan 6.2 — wato kashi daya bisa uku na dukiyarsa — a rana guda.

Bloomberg ta bayyana cewa hannun jarin Lukoil ya yi kasa da kashi uku cikin 100 a ranar Alhamis da Rasha ta fara yakin.

Na biyu shi ne Alexey Mordashov, Shugaban kamfanin sarrafa tama na Severtal, wanda ya yi asarar Dala biliyan 4.2.

Vladimir Potanin, Shugaban Kamfanin Norilsk Nickel – kuma wanda yanzu ya fi kowa dukiya a Rasha – ya yi asarar Dala biliyan uku.

Ido na kan makusantan Putin

Rikicin na Ukraine, wanda shi ne mafi muni bayan Yakin Duniya II a nahiyar Turai yana barazana ga tattalin arzikin yankin, musamman Rasha.

Amurka da Birtaniya na shirin sanya takunkumi ga wasu attajiran Rasha da ke alaka da Shugaba Putin, ciki har da Gennady Timchenko.

Daraktan Shirin Rasha da Eurasia a Jami’ar Tufs Fletcher, Chris Miller, ya ce, “Takunkumin zai jigata su sosai, saboda mutane da yawa a Amurka da nahiyar Turai na so su taba su ne kai-tsaye.”

Bloomberg ta bayyana cewa a cikin shekara guda Alekperov da Timchenko sun yi asarar Dala biliyan 10 kowannensu.

Asarar da su biyun suka tafka a shekara guda ya kai kasha 40 na dukiyarsu, wanda shi ne mafi girma a sanin Bloomberg.