Shugabannin yankin Kudu-maso-Yammacin Najeriya sun kai wa Shugaba Buhari ziyarar ta’aziyyar rasuwar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10.
Tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Laftanar Janar Alani Akinrinade (murabus) na daga cikin masu ta’aziyyar da Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
- An yanke wa dattijo lafiyayyar kafa aka bar mai ciwon
- Majalisa ta yi wa kudirin soke bautar kasa karatun farko
- An kashe wadanda suka fasa gidan yarin Owerri
Tinubu da Cif Pius Akinyelure da suran masu ta’aziyyar sun isa Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ne a daren Talata domin jajanta wa Shugaba Buhari a yayin na Najeriya ke makokin rasuwar sojojin 11.
Sauran masu ta’aziyyar sun hada da tsohon Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa, Cif Bisi Akande da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Olusegun Osoba.
Janar Attahiru da wasu janar-janar hudu da wasu hafsoshi da kananan sojoji da ke cikin tawagarsa ta ziyarar aiki sun rasu ne a hatsarin jirgi saman soji ranar Juma’a a Kanduna.
A ranar Asabar aka yi musu jana’iza cikin alhini yayin da Fadar Shugaban Kasa ta ayyana makokin kwana uku.