✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atletico ta ɗauko Gallagher daga Chelsea

Tafiyar Gallagher na zuwa ne a daidai lokacin da Chelsea ta ɗauko ɗan wasan gaban Atletico Joao Felix.

Atletico Madrid ta ɗauko ɗan wasan tsakiyar Ingila, Conor Gallagher daga Chelsea a kan farashin da ake hasashen zai kai fam miliyan £33m.

Ɗan wasan mai shekara 24 ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyar da ƙungiyar ta La Liga.

Gallagher ya kasance a Chelsea ne tun yana ɗan shekara shida, sannan ya ci gaba da samun horo har ya kai ga fara buga wasa, inda ya buga wasa 90, sannan ya zura ƙwallo 10.

Kakar bana ce dai shekararsa ta ƙarshe a Chelsea, inda ƙungiyar ta sayar da shi domin gudun rasa shi a kyauta a kakar baɗi.

A kakar bara, Gallagher ya buga wa Chelsea wasanni 50, inda yake haskawa a wasannin a matsayin kyaftin sakamakon jinyar rauni da Reece James ya yi fama da ita.

A shekarar 2019 Gallagher ya lashe Gasar Europa a Chelsea, inda a yanzu ya raba gari da ita bayan haskawa a wasanni 95 da jefa ƙwallo 10.

Kazalika, Gallagher ta buga wa Ingila wasa 18 tun bayan da ya fara shiga ’yan wasan tawagar a 2021, kuma yana cikin ’yan wasan tawagar da suka je Gasar Kofin Duniya ta 2022, da kuma Gasar Kofin Nahiyar Turai ta 2024.

Tafiyar Gallagher na zuwa ne a daidai lokacin da Chelsea ta ɗauko ɗan wasan gaban Atletico Joao Felix.

Joao Felix, wanda shi ma shekarunsa 24 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekara 7 a Stamford Bridge.

Felix wanda tsohon ɗan wasan Benfica ne ya yi zaman aro a Chelsea a kakar 2022/2023 inda ya haska a wasanni 20.

Kyauta Joao Felix ya koma Chelsea, sai wasu gidajen jaridu na Birtaniya sun ruwaito cewa Chelsea ta amince da biyan farashin da kai aƙalla fam miliyan 40 domin ɗauko ɗan wasan.

A shekarar 2019 Joao Felix ya koma Atletico inda ya haska a wasanni 131 ƙarƙashin jagorancin Diego Simeone, amma ya yi zaman aro a Barcelona a kakar bara.