Tsohon Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya maida martani ga masu sukar shi kan zabo Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Ce-ce-ku-ce kan lamarin dai ya ki ci ya ki cinyewa a jam’iyar musamman ma jagororinta, in da har wasu sun fara kiraye-kirayen tsige Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Iyorchia Ayu.
- Maniyatan Najeriya 2,500 ba za su samu zuwa Hajji ba
- Bayan korar malamai 2,000 El-Rufai zai dauki wasu 10,000
Alamu dai na nuna jam’iyar na fama da masassarar siyasa, wanda har ya janyo gwamnonin jam’iyar 11 daga cikin 13 suka kaurace wa taron da kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyar gabanin zaben Gwamnan Jihar Osun ranar Laraba.
Da yake maida martani kan lamarin, Atiku ya ce suna nan suna duba hanyoyin da za a bi wajen warware matsalolin jam’iyar a halin yanzu.
“Jam’iyar PDP za ta ci gaba da kasancewa a hade, abin da muke bukata kawai shi ne maida hankali kan abubuwan da muka sanya a gaba.
“Hadin kan jam’iyarmu ya fi komai muhimmaci a gurina, domin idan muka gaza hada kan ’ya’yan jam’iya ta yaya za mu hada kan ’yan Najeriya?”, in ji Atiku.
A shafinsa na Twitter, Atikun ya ce “Kowanne Gwamna ko dan majlisa da masu rike da mukamai da sauran ’yan jam’iyarmu da magoya bayanmu masoya ne a gare ni, kuma ina girmama su, ina sauraron su kuma mun dauki matakin da ya kamata, za kuma mu ci gaba da dauka daga nan har illa masha Allahu”.