Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da yada labaran karya a kansa.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE, Atiku ya ce bai zabi Wike a matsayin abokin takararsa ba saboda yana son wanda zai iya yin aiki tare da shi cikin aminci.
- Gumi ya caccaki Gwamnati kan barazanar daukar mataki a kan Daily Trust da BBC
- Yadda ICPC ta gano Naira miliyan 540 a asusun malamar Firamare
“Ba wanda yaki amincewa da gwamna Wike. Babu wanda aka ki amincewa da shi a cikin jam’iyya.
“Amma dole ne ku fahimci cewa hakkin dan takara ne ya zabi abokin takararsa – wanda ya yi imanin zai iya yin aiki tare da shi cikin lumana, sannan kuma ya fitar da manufofin jam’iyyar, da kuma kokarin hada kan kasa.
“Gwamna Wike hazikin dan siyasa ne. Yana da karfin hali da jajircewa. Na yi imani yana da makoma a siyasar kasar nan. Ba batun kin amincewa ba ne. Tabbas, ina ganin abu ne mai tsauri da za a ce mun ki amincewa da gwamna Wike,” in ji Atiku.
A martanin da ya yi wa Atiku, Wike ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su san gaskiyar abubuwan da suka faru a lokacin zaben fidda-gwanin da jam’iyyar ta gudanar.
Da yake magana da manema labarai bayan dawowa daga baluguron da ya yi zuwa kasar Spain a ranar Juma’a, Wike ya zargi Atiku da yi masa karya, yana mai cewa zai sanar da gaskiyar lamarin da ke faruwa a jam’iyyar.
“Na yanke shawarar yin shiru ne saboda PDP jam’iyya ce da nake matukar so. Na ci gaba da kulla yarjejeniya ta zamantakewa da mutanen Ribas. Duk da haka, lokaci ya yi da za a sanar da ‘yan Nijeriya gaskiyar abin da ya faru.
“Ni ba bawa ba ne kuma ba zan zama bawa ba. An haife ni da ‘yanci a kasar nan,” in ji shi.
PDP ta fada rikicin cikin gida
PDP ta fada rikicin cikin gida bayan kammala zaben fidda-gwanin takarar shugaban kasa wanda Atiku ya zama zakara.
Atiku ya kayar da Wike a zaben fidda-gwanin da aka yi kuma jam’iyyar ta gabatar da tayin a zabi gwamna Wike a matsayin abokin dan takararsa, amma Atiku ya zabi gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
Zabin Atiku ya haifar da cece-kuce a tsakanin shugabancin PDP, sai dai gwamnan na Ribas ya rufe bakinsa kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda-gwanin.
Kazalika Wike ya gudanar da tarurruka da dama da shugabannin jam’iyyar APC da sauran jam’iyyu, inda ya nuna damuwarsa kan makomarsa da babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya.
Wike ya caccaki jawabin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a ranar da ya bayyana gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.
Ya kuma zargi tsohon mataimakin shugaban kasar da yi masa kage. yana mai cewa Atiku na ribatar wasu jiga-jigan babbar jam’iyyar adawa wajen yada karya a kan mutanensa.
Gwamnan ya sha alwashin mayar da martani ga Atiku da ‘yan barandarsa daya bayan daya.