Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi tir da kisan Dan Birtaniya mai yada addinin Kirista mai suna Lan Squire da masu garkuwa da shi suka yi a jihar Delta.
Wazirin Adamawar ya yi Alla-wadai da lamarin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ta ofishinsa da ke hulda da manema labarai a Abuja.
Ya bayyana batun da abin tsoro kuma abin kyama bayan sakin masu taimaka masa sai masu garkuwar suka kashe shi.