Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya jagoranci bude makarantar haddar Alkurani a garin Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Makarantar wacce Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya gina dai an sanya mata sunan kakansa, wato Gwani Muhammadu Dan Gunduwawa.
- Zaben 2023: Gwamnati ta ba jami’o’in Najeriya hutun mako 3
- Kansiloli sun tsige Shugaban Karamar Hukuma a Kano
Za ta dauki dalibai 500 da suka kunshi maza 250 da mata 250 da za su yi karatu a lokaci guda wanda kuma ake sa rai za su haddace Alkurani a cikin wata shida.
Yayin da yake jawabin a wajen bikin bude makarantar tsohon, Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yaba wa Sanata Shekarau kan wannan aiki da ya yi inda ya ce makarantar za ta taimaka kwarai wajen ciyar da Ilimi addini gaba
Wazirin na Adamawa ya zo Kano ne don kaddamar da yakin neman zabensa na Shugaban Kasa a Jihar.
A nasa bangaren Sanata Shekarau ya gode wa Atiku Abubakar bisa bude masa makarantar da ta yi.
A cewar Shekaru dama a kullum yana tunani kan yadda al’umma za su sharbi romon Dimukuradiyya ta hanyar samar da ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma har ma da wadanda za a haifa a nan gaba.