✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

ASUU ta janye yajin aiki na wucin gadi

Kungiyar ta dakatar da yajin aikin ne domin yanke shawara kan umarnin kotu na ta koma bakin aiki

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a Najeriya.

Kungiyar ASUU ta amince ta janye yajin aikin ne a babban taronta na Majalisar Zartarwa da ya gudana a Abuja, wanda shugabannin rassanta da sauran manyan jami’ai suka halarta.

A safiyar Juma’a, lauyan kungiyar, Femi Falana, ya ce, “An amince da janye yajin aikin ne a cikin dare, yau da safe ASUU za ta yi taron manema labarai a Abuja ta sanar a hukumance.”

Shi ma wani babban jami’in ASUU da ya halarci taron ya  ce, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Nan gaba da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwa a hukumance,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Janye yajin aikin ASUU na zuwa ne wata takwas cif ke bayan malaman jami’o’in gwamnati a fadin Najeriya sun bi umarnin uwar kungiyar na daina aiki daga ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022.

Da sauran rina a kaba

Shugabannin Kungiyar sun amince su dakatar da yajin aikin ne a taron da suka fara a cikin dare zuwa wayewar garin Juma’a ne, domin su yanke shawarar matakin da za su dauka kan umarnin kotu.

A makon jiya ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta bai wa kungiyar umarnin janye yajin aikin da aka shafe wata takwas malaman jami’o’in gwamnati ba sa aiki.

Dalilin yajin aikin ASUU

Malaman sun shiga yakin aikin bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawuran da ta yi musu game da biyan hakkokinsu da suke bi bashi da kuma alkawuran da ta yi musu a jarjejeniyar da bangarorin suka rattaba hannu a 2009.

Baya ga bukatun da suka danganci inganta harkokin karatu da bincike a jami’o’in gwamnati, bangaren biyu na takaddama kan batun tsarin albashi na bai-daya na IPPIS da gwamnati ke biyan ma’aikata.

ASUU ta ce IPPIS na tauye hakkokin mambobinta, don haka dole a bari su ci gaba da tsarin albashi na UTAS da jami’o’i suka fitar wa ma’aikatansu.

Sai dai gwamnati ta ce allambaran, dole lakcarorin, kamar kowane ma’aikacin gwamnati, su koma karbar albashi ta IPPIS.

Kwan-gaba-kwan-baya

An dade ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin, har ta kai ga Shugaban Kasa Buhari ya umarci Ministan Ilimi ya shiga batun ya kuma ba shi wa’adin shawo kan lakcarorin; Amma duk da haka tana kasa tana dabo.

Gabanin haka, zaman da kungiyar ta yi ta yi karkashin jagorancin Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya gaza samar da kyakkyawan sakamako.

Hasali ma, lakcarorin sun ya karyata ikirarin Ngige na biyan wasu bukatunsu, suna masu nuna rashin sakankancewa da alkawuran gwamnati.

Akalla sau biyu ASUU na cewa ta kara wa gwamnati wa’adin da ta dibar wa kanta domin tattaunawa don yanke shawara a kan bukatun masu yajin aikin.

Zuwa kotu

Daga baya dai, bayan lallashi da alkawuran gwamnati ta gaza shawo kan ASUU, gwamnati ta maka kungiyar a Kotun Kwadago, wadda a karon farko ta umarci kungiyar ta koma bakin aiki.

Rashin gwamsuwa da hukuncin ya sa kungiyar garzayawa zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayyan wadda ta tabbatar da hukuncin kotun farko.

Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin ne bayan shawarar da ta bai wa bangarorin na sasantawa a wajen kotu ya ki amfani.

Ana cikin haka ne a baya-bayan nan ne Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga lamarin, inda cikin ’yan kwanaki zaman ya fara nuna alamar haske.

A yayin da Majalisar ke sauraron bangarorin, ASUU ta kara zargin IPPIS da rashin inganci da kuma tauye wasu hakkokin lakcarori.

Sai dai a yayin zaman, Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani ta Kasa (NITDA) ta shaida wa Majalisar cewa ta yi wa UTAS gwajin inganci a akalla sau biyu, kuma tsarin na gazawa.

Ta ce a duk lokacin da ta kammala gwaji takan sanya ASUU ta kara nazari da inganta tsarin, amma idan aka dawo aka yi wanin gwajin, sai ya fadi.

NITDA ta kuma sanar da gano wasu nakasu da gano a tattare da IPPIS.