Wata daliba ta bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta dakatar da kason wata-wata da aka saba bai wa Fadar Shugaban Kasa da ma’aikatu har ma da Gwamnoni har sai an shawo kan yajin aikin da malaman jami’a ke gudanarwa.
Shugabar Kungiyar Dalibai ta jami’ar Jihar Binuwai, Soohemba Agatha Aker, ce ta bukaci hakan a madadin daukacin takwarorinta da yajin aikin ya shafa.
Kazalika, cikin karar da lauyarta, Chukwuma Machukwu-Ume (SAN) ta shigar kotu a ranar 21 ga Satumban 2022, Aker ta sake neman kotu ta dakatar da albashi da alawus-alawus din duka Manyan Sakatarorin da na shugabannin hukumomin gwamnati da na shugabannin jami’o’in da suke yajin aiki.
Har wa yau, dalibar ta bukaci a dakatar da albashi da alawus din duka manyan jami’an jami’o’in da ke yajin aikin da na mambobin ASUU har zuwa lokacin da kotu za ta saurari kara da kuma yanke hukunci kan karar da ke gabanta.
Ta ce yayin da su dalibai ke cikin damuwa da gararamba a tituna, su kuwa suna can suna ci gaba da karbar albashinsu da alawu-alawus ba tare da wata mishkila ba.
Ta ce, “Abu ne da aka saba gani galibin ‘ya’yan shafaffu da mai a cikin al’umma, har da yaran ’yan siyasa da manyan jami’an gwamnati a kasar nan, ba sa zuwa kowace makaranta in ba ta kudi ba ko kuma a ketare.”
Don haka ta bukaci kotu ta dakatar da ayyukan Shugaban Majalisar Dattawa da na Shugaban Majalisar Wakilai, tara kudaden shiga, kason wata-wata da hukumomi suka saba samu da sauransu.
Ya zuwa yanzu dai kotun ba ta tsayar da ranar da za ta fara sauraron karar ba.