✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU: An ki bude azuzuwan dalibai a jami’o’in Kano

Har yanzu dakin kwanan dalibai mata na Jami’ar Bayero da ake kira Nana, cike yake da ciyayi.

Duk da janyewar yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU, azuzuwa da dakunan kwanan dalibai sun kasance a rufe a wasu jami’o’i a Jihar Kano.

Wannan lamari dai na faruwa ne duk da sanarwar da Jami’ar Bayero da kuma ta Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) suka fitar na ayyana Litinin a matsayin ranar komawa bakin aiki domin ci gaba da karatu.

A ziyarar da wakilanmu suka kai jami’o’in ranar Litinin, sun tarar da ma’aikata na tsaftace harabar jami`o`in da kuma dakunan kwanan daliban, domin shirin fara karatun a ranar 24 ga watan Oktoban da jami’o’in suka ba da sanarwar komawa aiki.

Sai dai duk da azuzuwan na rufe, ofisoshin ma’aikata marasa karantarwa na bude, inda suke gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba.

Fitaccen dakin kwanan dalibai mata na Jami’ar Bayero da ake kira da Nana, cike yake da ciyayi, sakamakon yajin aikin watanni takwas da ASUU ta yi.

Wata daliba da Aminiya ta tarar a dakin kwana daliban mai suna Rakiya Musa ta ce tuni ta koma dakinta domin taya ma`aikatan tsaftace shi kafin dawowa ranar Litinin din.

“Na zo ne domin tsaftace dakinmu, domin ina fatan kwaso kayana na dawo nan da kowane lokaci”, in ji Rakiya.

Daga Salim Umar Ibrahim Kano da Sadiq Adamu (Kano) da Rahima Shehu Dokaji