✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asirin mace mai ba da asirin bacewa ya tonu a Katsina

Dubun wata mata mai suna Hassatu Isa mai shekara 30 da ke Jibiya a Jihar Katsina wadda ta yi ikirarin tana bayar da asirin bata…

Dubun wata mata mai suna Hassatu Isa mai shekara 30 da ke Jibiya a Jihar Katsina wadda ta yi ikirarin tana bayar da asirin bata da kariya mai karfi ya cika yayin da ta kasa bace wa komar ’yan sanda a jihar. Hassatu wadda ta ce tana da asiran da take bayarwa ciki har da na bacewa, inda ta ja ra’ayin wani mai suna Rabi’u Haruna mai shekara 30 ana zargin ta yaudare shi ta karbi Naira miliyan daya da dubu 992 da nufin za ta ba shi layar bata da ta kariyar jiki. Hassatu wadda ake zargi da yin tsafi ta samu sabani da Rabi’u ne bayan gaza cika alkawarin da ta yi masa na ba shi wancan asiri. Ganin akwai yaudara da Hassatu take yi masa ne sai Rabi’u ya nemi ta mayar masa da kudinsa inda nan ma’amular tasu ta canja salo. Maimakon daukar matakin warware matsalar ta hanyar sulhu, sai aka zargi Hassatu ta dauki  hanyar raba Rabi’u da duniyar baki daya ta hanyar bayar da kwangilar kashe shi ga wani wanda ake zargin ya kware a  harkar ina-da-kisa mai suna Babangida Dalha shi ma mai shekara 30 mazaunin Jibiya, inda aka yi zargin ta biya shi Naira dubu 50 ya yi wannan aiki.

Bincike ya gano cewa bayan kama  Babangida, kafin hakarsa ta cimma ruwa , Babangida ya ce ya yi amfani da guba don aika Rabi’u zuwa Lahira amma sai duk shirin da ya yi ya wargaje. A yanzu haka dai wadanda ake tuhumar suna hannun ’yan  sandan Jihar Katsina ana ci gaba da bincike, kamar yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Sanusi Buba ya ce lokacin da ake gabatar da  wadanda  ake zargin ga manema labarai a Hedkwatar Rundunar da ke Katsina.

A wani labarin kuma, wani mai suna Sani Ibrahim na garin Moniya da ke Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina wanda ake yi wa lakabin ‘Kwalba’ wanda ake zargin kwararre wajen gyarar bingida ya shiga hannun ’yan sanda bisa tuhumarsa da ake yi da garkuwa da mutane. ’Yan sandan na tuhumar Sani da sace wadansu mutum biyu  masu suna Dahiru Bello da Malam Tashi dukkansu mazauna kauyen Salihawa da ke Karamar Hukumar Safana, inda ake zargin ya bukaci da biya shi Naira dubu 500 kafin ya sako su. Sani Kwalba ya shiga hannu ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a wurin da ake zargin maboyarsu ce.