✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asirin gwamnan da ya saci Naira biliyan 60 ya tonu

EFCC ta gano yadda gwamnan ya wawure kimanin Naira biliyan 60 daga asusun jiharsa.

Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta ce ta gano wani gwamna daga Arewacin Najeriya, da ya saci biliyan 60 daga lalitar gwamnatin jihar.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan sai dai bai bayyana sunan gwamnan ko jihar da aka saci wadannan makudan kudi ba.

“Zan iya fada muku a kyauta cewa sabon sashen da muka bude kan leken asiri yana aiki tukuru; Ya kuma bankado abubuwa da dama.

“Daya daga cikinsu shi ne gwamnan wata jiha a Arewa Ta Tsakiya da muka gano cewa a cikin shekara shida da suka gabata, ya cire zunzurutun kudi da suka kai kimanin Naira biliyan 60.

“Muna bibiyar abubuwan da yake yi kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da ’yan Najeriya abubuwan da muka yi a bayan fage game da laifukan da ake aikatawa ta amfani da shafukan intanet…,” a cewar Bawa.

Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da hukumar take aike wa manema labarai duk karshen wata.

Tun bayan maye gurbin tsohon shugaban hukumar Magu da Bawa ya yi, ana ta jinjina masa kan irin sabon salon aiki da hukumar ke amfani da shi wajen yaki da rashawa a Najeriya.