✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asibitin Malam Aminu Kano na neman taimako don kafa cibiyar masu ciwon zuciya

Hukumar Gudanarwar Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ta nemi gwamnatoci a dukkan matakai su tallafa wa asibitin don samar da cibiyar kula da masu…

Hukumar Gudanarwar Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ta nemi gwamnatoci a dukkan matakai su tallafa wa asibitin don samar da cibiyar kula da masu fama da cutar zuciya.

Shugaban Tsangayar Koyar da Aikin Likita na Jami’ar Bayero Farfesa Mahmud Umar Sani ne ya yi wannan kira a taron lalubo hanyoyin magance cutar zuciya da hukumar asibitin da Kungiyar Likitocin Birtaniya da Saudiyya suka shirya a Kano.

Farfesa Mahmud Sani ya kara da cewa masu ciwon zuciya a kasar nan musamman a Jihar Kano suna shan wahala a wasu lokuta ma sukan mutu sakamkon tsadar da aikin zuciyar ke da shi, “Lura da tsadar da aikin ke da shi ya sa muka ga ya dace mu zaburar da gwamnati da kungiyoyi masu taimakawa a duniya da masu hannu da shuni su zo a hada karfi don a samar da wannan cibiya a cikin wannan asibiti,” inji shi.

Ya ce duk da cewa aikin samar da cibiyar abu ne da zai dauki lokaci amma asibitin zai yi kokarin samar da duk kayayaykin da a yanzu haka ba ya da su don taimakon masu wannan cuta.

Shi ma wani kwararren likitan zuciya a asibtin, Dokta Isma’il Jamil Ahmad ya bayyana cewa kasar nan na fama da karncin cibiyoyin kula da cutar zuciya wanda ya janyo masu lalaurar ke mutuwa, “A Arewacin Najeriya babu irin wadanann cibiyoyi kuma ga shi ana ci gaba da haihuwar yara da ke da wanann cuta. A yanzu haka bincike ya nuna cewa a kasar nan duk shekara ana haihuwar yara kimanin dubu 52 masu dauke da ciwon zuciya inda kuma kashi biyar daga cikinsu ke mutuwa sakamakon rashin samun kulawar da ta dace,” inji shi.

A wani labarin kuma Asibitin Malam Aminu Kano ya bukaci kamfanoninn da ke sarrafa magunguna su rage wa asibitocin gwamnati farashin magunguna kamar yadda suke yi wa asibitoci masu zaman kansu.

Shugaban riko na Asibitin Farfesa Abdurrahaman Abba Sheshe ne ya yi wannan roko yayin da ya karbi bakuncin shugabannin sashen kasuwanci na kamfanonin magunguna na duniya.

Farfesa Abdurrahman Sheshe ya kara da cewa farashin magunguna a asibitocin Gwamnatin Tarayya ya fi na shaguna, inda hakan ke matsayin barazana ga harkokin tafiya tare da karya dokokin sayar da magunguna.

Ya bukaci kamfanoni da kungiyoyi su hada kai wajen cinikayyar magunguna a asibitoci domin saukaka wa al’umma kasancewar gwamnati kadai ba za ta iya biyan bukatun al’umma da harkokin lafiya ba.

Da take jawabin a madadin bakin, Misis Toyin Mylan ta ba asibitin tabbacin za su rika samar masa da magunguna da sauran kayan aikin lafiya cikin sauki.