✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe yana gani

Ashe yana ganiWata rana fada ya hada kurma da makaho, suna cikin fadan ashe akwai mutane a wurin. Idan kurman ya buya sai su fada…

Ashe yana gani
Wata rana fada ya hada kurma da makaho, suna cikin fadan ashe akwai mutane a wurin. Idan kurman ya buya sai su fada wa makahon cewa ya kai duka waje kaza. Kan haka sai aka yi sa’a kuwa in ya kai dukan ba ya samunsa. Da kurma ya ji abu ya yi yawa sai ya fice a guje yana cewa: “Shege ashe yana gani!”
Daga Mudassir Meshayi Bakin Tasha Ningi

Bawan sarki
Wani Babarbare ne bawan sarki, wata rana ya ci abinci ya koshi sai ya ce: “Alhamdu lillahi, yanzu na tabbata babu sarki sai Allah.” Da ya juya bayansa sai ya hada ido da dan sarki, sai ya ce: “Sai kuma uban wannan!”
Daga Laminu Umar Abba, 08131364647

Talauci ya yi rana
Wani Bafulatani ne zai hau mota a tasha sai kudinsa ba su cika ba sai aka ki yi masa ragi. A nan aka bar shi a tasha, mota ta tafi. Motar na cikin tafiya sai ta yi hatsari, wasu suka mutu wasu suka ji ciwo. Da aka dawo da su, Bafulatani ya tambayi abin da ya faru sai aka fada masa yadda hadarin ya faru. Budar bakin gogan naku ke da wuya sai ya ce: “Kan uba! Aradu yau talauci ya yi rana!!”
Daga Mustapha Bashir Yahuza Malumfashi, 07065635644

Riba da faduwa
Wani barawo ne ya je sata gidan wata tsohuwa. Bayan ya yi sa’a ya saci akuyarta ya kai kasuwa ya saida Naira dubu shida, sai ya laluba jakarsa domin ya hada kudin da na aljihunsa, ashe ya yi rashin sa’a, ya zubar da Naira dubu ashirin a gidan tsohuwa. Fitowar tsohuwa ke da wuya sai ta ga ba akuya amma ga daurin kudi a aje kusa da tirken akuya. Tsohuwa ta dauka ta gode wa Allah. Bayan jimawa sai ga barawon ya dawo gidan, ya tarar da tsohuwa zaune tana kirga kudi, sai ya yi karfin halin gaishe ta, ta kuma amsa masa. barawo ya ce mata: “Wallahi kaka, akuyar ma dubu shida aka saida ta. Sai ta ce: “Eh, haka sha’anin kasuwa yake, yau riba gobe faduwa!”
Daga Abdullahi Lawal danbaba kayauki, Katsina