✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe qarya ba daxi?

Ashe qarya ba daxi? Wani mutum ne yana da jika, shi ma jikan yana da aboki. To, wata rana tsohon nan ba shi da lafiya…

Ashe qarya ba daxi?

Wani mutum ne yana da jika, shi ma jikan yana da aboki. To, wata rana tsohon nan ba shi da lafiya sai jikan da abokinsa suka zo gai she shi. Bayan sun gaida shi sai suka fara hira sai kakan ya ce: “Ai har na tuna wata rana da muna samari, saboda tsabar shan sholisho idan kekena ya yi faci ba na kai wa wurin faci, da kaina nake yi. Kuma ba na sayen sholisho, kawai ina gama goge wurin sai dai kawai in yi kaki na tofa, kawai sai in liqa facin na manne wurin.” Yana gamawa sai abokin jikansa ya ce: “Ai ni ma har na tuna lokacin da kakana yake shaye-shaye, idan ya tashi shaye-shayensa, to injin niqa yake samu ya kafa kansa; sai ya wuni kafin ya xago kansa, ya fesa hayaqin sama.” Tsohon sai ya ce: “Kai yaro, wane kakan naka, abokina ne fa?” Sai yaro ya ce: “Ashe kaka qarya ba daxi?”

 

Ashe da biyu…

Wani mutum ne yake zuwa wajen wani wanzami, sai ya tambaye shi: “Wai zai kai kamar wane lokaci, kafin in samu aski?” Sai ya ce zai kai awa xaya, sai ya tafi. Wata rana ya sake dawowa ya ce: “Zai kai kamar awa nawa kafin in samu aski?” Ya ce awa uku, sai ya tafi. Haka ya riqa yi har kusan mako xaya. Rannan bayan zo ya yi tambayarsa kamar yadda ya saba, ya tafi sai wanzami ya ce wa wani abokinsa: “Ka bi bayan mutumin nan ka ga ina yake zuwa haka, domin idan ya zo ya tambaye ni, ba ya dawowa.” Da abokin nasa ya dawo sai ya riqa dariya. Wanzami ya ce: “Me ya ba ka dariya?” Sai ya ce: “Ai kullum idan mutumin nan ya bar nan, gidan matarka yake zuwa.”

Labarai Daga Yakubu Adamu Ningi, 09021109997

 

Raba gardama

Wani direban kiya-kiya ne da kwandastansa, kullum ba su jituwa. Ga su dai abokan juna amma shi direban ya raina kwandastan nasa, saboda ya yarda cewa Kwandastan nasa daqiqi ne ajin qarshe. Wata rana suna cikin aiki, sun xauko fasinjoji, kawai sai ta haxo su. Ai kuwa sai direba ya fara ce wa kwandastansa: “Jahili, daqiqi!” Shi kuma kuma Kwandastan yana cewa: “Wallahi ni ba jahili ba ne kuma ba daqiqi ba.” Wani fasinja da ke cikin motar ya shiga maganar ta hanyar nusar da direban da cewa ya daina kiran yaron motar da jahili. Ai kawai sai direban ya ce: “Na tabbatar maka da cewa shi jahili ne?” Fasinja ya ce yana son a nuna masa shaidar haka. Sai direba ya ce wa kwandasta: “Xaya a tara da xaya, faxa mana amsar.” Kwandasta cikin sauri don ya burge fasinjojin da ke motar sai ya amsa da cewa: “Goma sha xaya!” Ai kuwa kafin fasinjoji su bushe da dariyar wannan wauta ta kwandasta sai direban cikin sauri ya ce: “Wallahi wani ne cikin motar nan ya faxa maka amsar!”