✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe ni sananne ne a Kaduna?

Wani dan kabilar Igala ne (Gara) ya je Kaduna bakunta, sunansa Sabo. Da ya fita wajen Kasuwar Abubakar Gumi, sai ya ji masu bas-bas suna…

Wani dan kabilar Igala ne (Gara) ya je Kaduna bakunta, sunansa Sabo. Da ya fita wajen Kasuwar Abubakar Gumi, sai ya ji masu bas-bas suna cewa; Sabo, Sabo, Sabo, (suna nufin Unguwar Sabon Tasha), shi kuma sai ya dauka shi ake kira. Da an ce Sabo, sai ya waiwaya yana daga hannu. Da ya koma gida sai ya rika cewa “Ashe ni sananne ne a garin Kaduna? Domin da na je kasuwa duk inda na waiga sai na ji ana cewa, Sabo, Sabo, Sabo!”