✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe kuna gani

Wani matashi ne ya yi shaye-shayensa, kawai sai ya shiga wani shago, alhali mai shagon yana ciki, masu sayayya na ta harkoki, sai kawai ya…

Wani matashi ne ya yi shaye-shayensa, kawai sai ya shiga wani shago, alhali mai shagon yana ciki, masu sayayya na ta harkoki, sai kawai ya dauko kwali ya dinga zuba kaya. Mai shago ya tsaya yana ta kallonsa, masu sayayya kuma sun zaci ko yaronsa ne. Da ya cika kwalin ya dauka zai fita sai mai shagon ya riko rigarsa ya ce: “Kai, me kake nufi?” Yana waigowa sai ya ce: “Da ma ashe kuna gani na?”
Daga Sunusi Uban Kulob Garko-Kano 07038766018