✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asamoah Gyang zai bude kamfanin jirgin sama

Shahararren dan kwallon kasar Ghana Asamoah Gyang ya kammala shirye-shirye don bude wani katafaren kamfanin zirga-zirgar jiragen sama a Ghana. Gyang yana daya daga cikin…

Shahararren dan kwallon kasar Ghana Asamoah Gyang ya kammala shirye-shirye don bude wani katafaren kamfanin zirga-zirgar jiragen sama a Ghana.

Gyang yana daya daga cikin ’yan kwallon da suke da arziki a Nahiyar Afirka inda rahotanni suka nuna yanzu haka yana samun kudin shigar da suka kai Dala Miliyan 30 kwatankwacin Naira Biliyan 10 da Miliyan 800 ne a duk shekara.

Kamar yadda wata jarida mai wallafa labaran kasuwanci Business Insider Sub Saharan Africa ta kalato ta ce tuni dan kwallon ya samu lasisin bude kamfanin da ake kyautata zaton a Ghana ne zai bude.

Sai dai kamar yadda rahoton ya nuna, jirgin nasa zai fara ne da yin jigilar kaya a ciki da wajen Ghana kafin daga bisani ya tsunduma harkar  jigilar mutane.

Kamfaninsa da ke yunkurin fara yin zirga-zirgar jiragen sama ne ya tabbatar da samun lasisin fara yin zirga-zirgar daga Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama na kasar Ghana a wata sanarwa da ya fitar a shekaranjiya Laraba.

Gyang, dan shekara 31, an ruwaito yana daga cikin ’yan kwallon da suka fi samun kudi a duniya kuma an shaide shi wajen zuba jari a bangarori daban-daban na kasuwanci.

Kawo yanzu dan kwallon ya zuba jari a bangaren sufuri da na gine-gine da na saye da sayar da gidaje da gidajen mai da kuma a bangaren masana’antu.

Gyang ya buga wa kulob da dama a Turai da suka hada da Udinese na Italiya da Rennes na Faransa da Sunderland na Ingila inda yanzu haka yake kwallo a kulob din Kayserispor na Turkiyya.