Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Arsenal da ke Ingila sun nuna koci Unai Emery ya yanke shawarar sayar da Mohammed Elneny don ya samu sukunin sayo dan kwallon kulob din Villareal da ke Sifen Pablo Formals.
Elneny wanda tun da aka fara kakar wasa ta bana bai bugawa Arsenal wasa ko daya ba a karkashin sabon koci Emery, mahukunta kulob din sun yanke shawarar sayar da shi ne don maye gurbinsa da wani.
Kamar yadda jaridar The Sun da ake wallafata a Ingila ta kalato a shekaranjiya Laraba, ta ce, kulob din Arsenal ya ki sabunta kwantaragin Aaron Ramsey wanda zai tafi a karshen kakar wasa ta bana, kuma tana da burin maye gurbinsa ne da dan kwallon tsakiya a kulob din Villareal Pablo Formals don haka take yunkurin sayar da Elneny don amfani da kudin wajen yin cefanen.
An kiyasta Arsenal za ta kashe kimanin Fam Miliyan 18 kwatankwacin Naira Biliyan 8 wajen sayo Pablo mai shekara 22 daga kulob din Villareal.