✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal da Emirates sun sabunta yarjejeniya

Kamfanin jirgin sama na Emirates, ya sabunta yarjejeniya a tsakaninsa da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kan daukar nauyin tufafin kulob din, inda Arsenal da…

Kamfanin jirgin sama na Emirates, ya sabunta yarjejeniya a tsakaninsa da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kan daukar nauyin tufafin kulob din, inda Arsenal da Emirates suka tsawaita yarjejeniyar zuwa shekara biyar a ranar Litinin da ta gabata.

Y arjejeniyar ta kai ta Fam miliyan 200, sama da Naira biliyan 80 ta Najeriya, inda Arsenal za ta ci gaba da amfani a sunan Emirates a tufafinta har zuwa karshen kakar wasa ta 2023/2024.

Yarjejeniyar daukar nauyin tufafin ita ce mafi girma da Arsenal ta taba amincewa, kuma kawancen Arsenal da Emirates da aka fara a shekarar 2006 yanzu za ta kai zuwa akalla shekara 18.

Arsenal ta ce yarjejeniyar ci gabanta ce ta fuskar zuba jari kuma kamfanin Emirates zai taimaka wa kungiyar ga kishirwar lashe kofi.

A karkashin sabuwar yarjejeniyar, Arsenal za ta yi amfani da jiragen Emirates a lokacin wasannin share-fage na kakar wasanni. Sannan filin wasa na Arsenal zai ci gaba da amfani da sunan Emirates har zuwa shekarar 2028, a karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince a shekarar 2012.

Yarjejeniyar ta tsakanin Arsenal da Emirates ita ce mafi girma a Ingila, amma har yanzu akwai tazara a tsakaninsu da kawancen da ke tsakanin kulob din PSb Eindhoben na Holland da kuma kamfanin Philips.