Ariel Castro, dan shekara 53, wanda aka yanke wa hukuncin shekara dubu da daya, bisa laifin boye ’yan mata, har tsawon shekara 10, ya hallaka kansa. Mamacin wanda aka killace a wani gidan gyara halinka da ke garin Columbus a tsakiyar birnin Ohio, a cewar mai magana da yawun wannan cibiya ta gyara halinka, JoEllen Smith ya tabbatar da an samu mutumin a rataye, inda jami’an kula da lafiyar ’yan fursuna suka yi ta kokarin farfado da shi, amma kafin su karasa zuwa asibiti Castro ya cika.
An killace shi a wannan gida ne, domin munin laifinsa, kuma ana bibiyar halin da yake ciki a kowace rabin sa’a. ’Yan matan da ya boye, ya sace su ne a shekaru daban-daban, wato a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004. Kuma wadannan ’yan mata uku shekarunsu a lokacin da suka bace sun kama daga ’yar shekara 14 da 16 da 20. Sun tsira daga hannun Castro ne a ranar 6 ga Mayun bana.