✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume

Ndume, ya ce Arewancin Najeriya ba zai zamar wa wani yanki wahala ba.

Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno, ya ce Arewacin Najeriya na iya tsayawa da kafafunsa a ɓangaren tattalin arziƙi ba tare da dogaro da sauran yankuna ba.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce duk da cewar kowace jiha da yanki na buƙatar juna domin ci gaba, Arewacin Najeriya ba zai ɗorawa kowane yanki nauyi ba.

Ya mayar da martani ne kan wasu maganganu da ke cewa Arewa ba za ta iya tsayawa ba tare da taimakon sauran yankuna ba, kuma wai ’yan Arewa ba sa son biyan haraji.

“Arewacin Najeriya ba zai taɓa zama mai dogaro da wani yanki ko ma ƙasa baki ɗaya ba. Muna da muhimmanci ga Najeriya, ba ma ɗorawa kowa nauyi,” in ji shi.

Ndume, ya kuma musanta zargin cewa gyaran tsarin haraji na baya-bayan nan an yi shi ne domin cutar da Arewa, inda ya ce irin wannan tunanin bai dace ba.

Ya ce gyaran tsarin harajin ya shafi dukkanin ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi da matsakaicin ƙarfi.

Ya buƙaci Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS), da ta ƙara faɗaɗa hanyoyin karɓar haraji tare da inganta tattara kuɗaɗen.

Haka kuma, ya yi kira da a ƙara yin gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa kuɗaɗen haraji.