✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa maso Gabas ce mafi koma baya a Najeriya – Ndume

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya ce yankin Arewa maso Gabas da ya kunshi jihohin Adamawa da Bauchi da…

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya ce yankin Arewa maso Gabas da ya kunshi jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe, na cikin mawuyacin hali bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.

Alhaji Ali Ndume, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Maiduguri ya ce yankin na fama da matsalar talauci da rashin aikin yi ga matasa, ga kuma rashin kamfanoni da masana’antun gwamnatin tarayya da za su inganta tattalin arzikin yankin.
Sauran matsalolin a cewarsa sun hada da rashin ingantattun hanyoyin sufuri da uwa uba rashin tsaron da ya addabi yankin.
Sanata Ndume ya ce, yadda yankin ke cikin wahala ya sa mutanen yankin ke tunanin cewa Gwamnatin Tarayya ta mayar da yankin saniyar ware, inda ya ce suna sa ran zaben Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, zai taimaka wajen magance matsalolin tare da bunkasa yankin.
“Janar Buhari ya san yankin, inda ya yi Gwamnan Soja a yanki lokacin yana dunkule a matsayin Jihar Arewa maso Gabas, saboda haka ya san matsalolinmu kuma ya san irin abubuwan da muke da su na arzikin kasa musamman ma’adinai kuma ba abin mamaki ba ne a ce matsalolin yankin Arewa maso Gabas sun warware, saboda shugabancin Janar Buhari,” inji shi.
Ya bukaci manyan jami’an gwamnatin Buhari da ’yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai su zama ja-gaba wajen bijiro da kudirin farfado da shiyyar, kasancewar sun san halin da take ciki na koma baya. Ya ce idan aka bce Buhari ne kadai zai yi komai, to aikin zai yi masa yawa, don haka dole sai an samu taimakon sauran jami’an gwamnati da suka fito daga yankin.
Ya bukaci a ba yankin Shugaban Majalisar Dattawa ko Majalisar Wakilai, inda ya ce a baya ko a rabon mukamai an mayar da yankin saniyar ware.
Da ya juya kan cika shekara daya na ’yan matan Chibok fiye da 200 a hannun ’yan Boko Haram, Sanata Ndume, ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ta gaza kubutar da yaran har tsawon shekara daya.
Don haka ya bukaci sabuwar gwamnati mai zuwa ta kokarta wajen magance wannan lamari, “Muna fata Allah Ya sa suna nan lafiya kuma Allah Ya kubutar da su, kuma Ya kawo mana karshen wannan bala’i da muke ciki,” inji shi.