✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa ba za ta manta da kisan Sardauna ba

Tarihi ba zai taba mantawa da gudunmuwar Sa Ahmadu Bello Sardauna ba, musamman yaddda ya bullo da shirinsa na bunkasa Arewa, ta yadda ya himatu…

Tarihi ba zai taba mantawa da gudunmuwar Sa Ahmadu Bello Sardauna ba, musamman yaddda ya bullo da shirinsa na bunkasa Arewa, ta yadda ya himatu wajen fitar da al’umma daga kangin talauci, don dora su a kan tafarkin rayuwa mai inganci. Da makiyan Arewa suka hanga, sai suka fahimci Gamji barazana ne ga boyayyar manufarsu. Don haka a ranar 15 ga Janairun 1966 aka aiwatar da juyin mulkin day a halaka Sardauna da Firayiminista Tafawa balewa.
Ba wani dalili da zai sa a kashe Sardauna ko Sa Abubakar Tafawa Balewa, domin abin lura a nan,masu juyin mulkin ba su kashe dan kabilar Ibo ko daya ba, wannan yasa ake ma juyin mulkin da lakabi da “Juyin mulkin Inyamurai” saboda mafi akasarin wadanda suka aiwatar da juyin mulkin, Inyamurai  ne. Misali, Babban wanda ya shirya juyin mulkin shi ne Manjo Chukumeka Nzeogu Kaduna, wanda shi ne ya yi wa Sardauna kisan gilla, sauran manjo da suka tara mai baya sun hada da : Ifeajuna da Okafor, da Ademoyega da sauransu. Bayan sun aikata kisan gillarsu, mutumin da ya zama shugaba kasa, shi ne, Manjo Janar J.T.U. Aguyi Ironsi. Da darewarsa ya fara kafa wata dokar soja,mai lamba 34, wadda a zahiri ta kara fito da aniyar wadanda suka aikata ta’addancin a fili. Domin da farko sun fara nunawa wai ba juyin mulki ba ne, illa sun aiwatar da juyin juya hali ne, kuma har zuwa yau,farfagandar da suke yi ke nan cewa, abin da ya faru a daren 15 ga Janairun 1966, juyin juya hali ne. Shi kuwa abin da ya faru a 27 ga Yulin 1966, juyin mulki ne, wannan dai karya ce kawai wadda ba ta da tushe.
To sai dai,duk da sojojin Arewa sun aiwatar da abin da ake ma lakabi da juyin mulkin ramuwar gayya, inda suka yi nasarar kashe Aguyi Ironsi, to an riga an yi wa Arewa mummunar illa. An kashe jigo, wanda ya dasa dambar da za ta kai Arewa tudun na tsira. An kashe garkuwar Arewa, an kashe mutumin da ya hana a danne Arewa dannewar har a bada.
Shirin bunkasa Arewa, wanda a Turancin Ingilishi aka yi wa lakabi da “Northernization policy,” ya tada wa makiyan Arewa hankali matuka, kuma har yanzu makiyan Arewa, ba sa son ko tunawa da Northernization policy,domin ya hana su mamaye Arewa, yadda suka ga dama. Da ba ai Northernization Policy ba, da yanzu mu bayi ne a Arewa, domin ko gadi ba za mu samu ba, duk  ’yan kudu za su cika ma’aikatun gwamnati da duk wasu muhimman wurare,to amma Sardauna ya ki, ya ce sam,bai yarda ba.
A yanzu haka,manyan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya,’yan Kudu ne,suka cika su.Su kuwa kamfanoni masu zaman kansu ko gadi, ba su daukar Hausa/Fulani. Idan ka je Abuja za ka ga an takaita irin aikin da Hausa Fulani za mu yi,wato yankar farce da tallace-tallace tsakiyar titi. Ba zancen Fatakwal da Lagos ko Ibadan.To idan da Sardauna bai aiwatar da shirin bunkasa Arewa, wand aa Turance aka yi wa lakabi da “Northernization policy” ba, to da a Kano da Kaduna da Katsina ba za mu samu komai ba, sai noman gargajiya kawai, ma’ana za su mallake aikin gwamnati da bankuna da Inshora da Jaridu da komai, sai dai mu ci gaba da noman rani irin na gargajiya wanda bai hana talauci da yunwa.
A tarihi mun gano dalilin da yasa Jam’iyyar NPC karkashin Sardauna ta yi adawa da kudirin Jam’iyyar AG, inda Anthony Enahoro ya daga kudirin da a baiwa Najeriya cin gashin kai,domin su mamaye komai,domin a lokacin Arewa ba ta da isassun ’yan boko da za su cike gurabun da za su samu a ma’aikatun gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, saboda haka Gamji ya kekasa ya ce sam, ba yanzu ba, sai an nuna.
Kishin Arewa zunzurutunshi ne,yasa Sardauna ya zama barazana ga makiyan Arewa masu kiranmu da sunayen batanci daban-daban.Suka fara kulle-kulle, inda suka hana kasar ta zauna lafiya, ta hanyar tada fitintinu lokacin kidaya da zabe kamar kidayar 1962/3 da zaben 1964 da na 1965,daga karshe dai sai da suka ingiza soja suka aiwatar da boyayyyar manufarsu, sannan hankalinsu ya kwanta.
Wani dalili da yasa makiyan Arewa suka sare katangar Arewa wato Sardauna,shi ne, yadda ya ki yarda a shigo cikinmu a raba kanmu.Tun lokacin da aka kirkiro shiyyar Kudu maso Yamma ta tsakiya (Mid Western Region} sakamakon rikice-rikicen da suka auku a Shiyyar Yamma, musamman a Jam’iyyar Yarabawa ta AG, da kuma koke-koken kananan kabilu da suka ce Yarbawa na danne su, suna murkushe su, Su Awolowo sun yi yunkuri matuka domin su hada Hausa Fulani da kananan kabilun Arewa, amma ba su yi nasara ba,domin Sardauna ya dakile duk wata kafa. Amma yanzu fa? An ce kada su ci tuwo,su raina Hausa,su kyamace duk wani abu na Hausa Fulani,da sauran farfaganda ta kiyayya wadda daga karshe ta yi tasiri, domin an raba kan ’yan Arewa.
Sardauna,yana da biyayya da da’a  domin dan sarauta ne,yana da tarbiyya da son addini, domin jikan Shehu danfodiyo ne,yana da son kare al’adun ’yan Arewa, domin yasan cewa duk ci gaban duniya yana cikin al’adun jama’a, da sun sake su, sun aro wasu, to kashinsu ya bushe.
Mafita kawai yanzu dole ne, a sake lale, a yi juyin juya hali na farfado da kyawawan al’adun Arewa kamar girmama na gaba, da’a gaskiya da kunya da rikon amana da aiki tukuru da sauransu.
Kwamared Bishir Dauda sabuwar Unguwa Katsina
Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka 08165270879