✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APO-7: Wasika daga Barzahu

A wannan mako mun shiga shafin facebook na fitaccen marubucin nan ne Dokta Aliyu U. Tilde inda muka dauko makalarsa mai take a sama. Ya…

Gidan da sojoji da jami'an tsaron SSS suka kashe mutane tara a Apo AbujaA wannan mako mun shiga shafin facebook na fitaccen marubucin nan ne Dokta Aliyu U. Tilde inda muka dauko makalarsa mai take a sama. Ya yi wa makalar take Apo-7: Wasika daga Barzahu. To amma washegari sai wadanda suka rasu suka koma 8. Wasika ce mai taba zukata da tunatarwa ga jama’a:
Assalamu alaikum,
Mu ne wadanda hukumomin kasarmu Najeriya suka yi wa kisan gilla, muna barci a masaukinmu a unguwar ’yan majalisa ta Apo a daren Juma’ar da ta wuce bayan mun dawo daga neman halaliyarmu.
Neman halal ya sa muka baro garuruwanmu. Akasarinmu masu tukin keke NAPEP ne. Da yake ba mu da makudan kudin da za mu iya biyan gidan haya a Abuja, ire-irenmu kan samu gidajen da ba a kare ba, mu rika ba masu gadi na goro don su bar mu mu fake a ciki da dare. In gari ya waye, sai mu watse, kowa ya je wurin sana’a. Da muke zaune gidan nan, ba mu san da wani dan iska a cikinmu ba, ko mai zaman banza, balle kuma dan ta’adda.
Tabbas maigidan ya zo mana ranar Laraba, ya ce mu fice masa daga gida kafin kwana bakwai. Ya yi mana barazanar cewa zai kawo sojoji su yi mana duk abin da suka ga dama in mun ki fita. Mun yi niyya mu fice kafin wa’adinsa ya cika. Don haka kowannenmu ya fara tunanin ina zai koma kafin cikar wa’adin. Ko kadan ba mu yi tsammanin wani abu mummuna zai same mu ba. Illa iyaka gininsa yake so; mun kuma yi niyyar bar masa shi. Ina mu ina ja da hafsan soja, balle wanda ba hausarmu daya da shi ba?
Ashe maigidan daga baya ya canja ra’ayi ya ga kwana bakwai sun yi masa nisa. Duk da haka, maimakon ya dawo ya ce mu fita a ranar, sai kawai ya turo mana sojoji ran Alhamis da dare. Abin da muka fara ji harbi daya. Tau! Wasunmu da barcinsu bai yi nisa ba suka farka, wasu kuwa kafin su san me ake ciki wuri ya yamutse. Harbi kake ji ta ko’ina babu kakkautawa. Wasu sun samu sun gudu. Da yawa an ji musu munanan raunuka a ka, wasu a kirji, wasu a kafafunsu. Mu kuwa da abin ya taho da karar kwana, aka kashe mu. Mun mutu. Ga mu nan a Barzahu, daga inda muke rubuto muku wannan wasikar.
Abin da kowannenmu ke tambaya a nan shi ne, me ya sa aka kashe mu? Shin, in da ba mu da zuciyar nema, ma fito cirani, mu bar iyalanmu, danginmu da abokanmu, mu zo inda ba dangin iya babu na baba, mu yi ta kara-kainar neman halal don mu aika wa iyalanmu a gida? Wannan shi ne laifinmu na farko. A kasarmu Najeriya, mai neman halal shi ne abin zunde, wulakantawa da nuna wa rashin gata.
Da mun shiga bangar siyasar gwamnoninmu ne, da yanzu muna da gidaje da motoci. Amma halal, ita ce ta kai mu ga barin inda muke da gata, muka zo birnin tarayya muka rika kwana a gidajen da ba a kammala ba, wadanda ba kofa, ba taga, sai ’yar tabarmar da muke shimfidawa da kayan sawarmu na tafi-da-gidanka a cikin leda-bag.
Mun kuma tambayi kanunmu: shin za a dauki bindiga a kashemu idan da mu masu hali ne, masu motoci da gidaje da mukami da abokai a madafan iko? kaddara da maigidan ya samu masu hannu da shuni sun mai da gidansa wajen fasikanci, me kuke jin zai yi? Tabbas murna da haka zai yi. Nan da nan zai inganta gidan ya sa masu gadi da masu karbar kudi hannun duk wanda ya zo amfani da wurin. Amma kasancewarmu talakawa, mun zame abin tsana a Abuja. Duk inda muka je korarmu ake yi kamar kuda. An ce Abuja birni ne na mawadata, ba a so a ga alamun talauci a ciki. Talauci ya zama hujja ta wulakanci a Abuja da sauran manyan garuruwa kamar Legas.
Amma in da an duba, sai a gane cewa ba mu muka dora wa kanmu talauci ba. Halin da muka samu kanmu a ciki ne. Da makarantu na da kyau da mun yi karatu mai amfani da masana’antu na aiki da iyayenmu sun ba mu ilimi mai inganci; da an ba noma da kiwo hakkinsu ta hanyar wadatar da al’umma da kayan noma kama daga ingantaccen iri zuwa kasuwar amfanin gonar, da ba mu baro karkarunmu muka zo inda ake ganinmu kamar marasa galihu ba. Don haka ba laifinmu ba ne. Duk da halin da muka samu kanmu a ciki, mun yi kokarin ingata rayuwarmu ta hanyar neman halal.
Bugu da kari, mun tambayi junanmu: Shin, anya kuwa da maigidan zai kira mana sojoji su kashe mu idan da a ce kabilarmu da shi daya ce? Da wuya, don kuwa jini ya fi ruwa kauri. Hausarmu ita ta kara tunzura sojan nan. Yau Bahaushe ya zama abin tsana tsakanin sauran ’yan Najeriya saboda dalilai da yawa. Wadansu na kishin yawan da Allah Ya ba mu; wasu na kishin addininmu; wasu na kishin arzikin kasa da albarkatunta da Allah Ya yi mana; da sauransu. Wasu kuma tsoronmu suke ji don sanin duk ranar da muka farka daga barci, za mu taka wa kowane dan iska birki. Wasu kuma na haushin mun ci su da yaki, walau a da kafin zuwan Turawa ko lokacin Yakin Basasa. Da sauran dalilai da wuri ba zai bar mu mu yi dogon bayani a kansu ba.
Wadannan dalilai su suka sa ake mana zagon kasa ta hanyoyi daban-daban musamman da yake mun yi sake an yaudare mu mun mika wa wasu mulki. Duk abin da za a yi a mai da mu baya ko a nuna mana wulakanci ya zama wajibi. Wa ya san adadin wadanda aka kashe da sunan Boko Haram, ba su san hawa ba, ba su san sauka ba? Hatta manyanmu, irin Janar Mamman Shuwa, an kashe a gaban sojojin da ke zaune a kofar gidansa amma ba su yi komai ba, aka ce wa duniya Boko Haram ne suka kashe shi!
Akwai maganar raini wacce ta bijiro daga rashin shugabanni masu kishin jama’arsu, wadanda suka fifita duniya a kan Lahira. Yayin da sauran al’ummomi a Najeriya ke da shugabanni da ke cara duk lokacin da aka taka hakkin mutanensu, mu shugabanninmu tsit kake ji! In an tambaye su sai su ce ai suna magana a bayan fage. Sun zame kamar Malam Zurke a cikin labarin Ruwan Bagaja wanda wani kato ya dauke matarsa da mari. Sai matar ta kalli mijinta Malam Zurke. Sai Malam Zurke ya ce wa katon nan ya sake marinta. kato ya sake kwashe ta da mari. Haka aka yi har sau uku. Sai Malam Zurke ya ce da matarsa su koma gida. A gida sai matar ta tambayi mijin yaya bai yi komai ba, yayin da ake ta marinta. Sai Malam Zurke ya ce ai a lokacin ya sa hannu cikin riga yana yi wa katon dakuwa ne!
Gaskiyar magana ita ce shugabanninmu sun sa duniya a gaba. Kowane ba aikin da yake yi da ya dogara da shi har da zai iya nuna wa gwamnati yatsa. Duk sun dogara da gwamnati, kowa na neman mukami ko kwangila ga kansa da ’ya’yansa. Lokaci ya wuce da ake tsoron a taba mu, lokacin da manyanmu suka rike gaskiya ba su damu da duniya ba. Har wani mawaki na cewa:
Ai Ana son a taba mu ’yan Arewa,Ana tsoron manyan mutane.Ku tashi mu farka ’yan Arewa Ku san barci aikin kawai ne.