✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi da Kansiloli a zaben Filato

Kazalika, jam’iyyar ta kuma lashe dukkan kujeru 325 na Kansilolin da ke Jihar.

Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Filato ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi 17 a zaben Kananan Hukumomin da aka gudanar a Jihar ranar Asabar.

Kazalika, jam’iyyar ta kuma lashe dukkan kujeru 325 na Kansilolin da ke fadin Jihar.

Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Filato Mai Zaman Kanta (PLASIEC), Fabian Ntung ne ya bayyana sakamakon da safiyar ranar Lahadi.

Sai dai rahotanni sun nuna zaben ya yi fama da karancin fitowar masu kada kuri’a.

Hakan dai ana ganin ba zai rasa nasaba da rashin tsayawar babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben ba, sakamakon wani hukuncin kotun daukaka kara da ya hana ta shiga zaben kan rashin bin ka’idoji wajen tsayar da ’yan takararta.

Wannan dai ya ba jam’iyyar APC damar lashe dukkan kujerun ba tare da wata hamayya ba.

Kotun dai ta tsayar da watan Nuwamba mai zuwa domin sauraron karar da PDP ta daukaka, ko da yake ba a san ko zata sami abin da take nema ba, kasancewar an riga kammala zaben tare da sanar da wadanda suka yi nasara.

Gwamnan Jihar ta Filato, Simon Lalong ya yaba wa al’ummar Jihar kan yadda suka gudanar da zaben lami lafiya ba tare da tarzoma ba.