✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da Obaseki zai kiyaye yayin zaben gwamna Edo —APC

Jam’iyyar APC ta kirayi Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo, da ya tabbatar kwanciyar hankali gami da adalci yayin gudanar da zaben gwamnan jihar a…

Jam’iyyar APC ta kirayi Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo, da ya tabbatar kwanciyar hankali gami da adalci yayin gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Satumba.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin Mista Patrick Obahiagbon, Mataimakin Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben APC na Kasa, yayin zantawa da ‘yan jarida ranar Juma’a a Abuja.

A cewar Mista Patrick, babu wanda burinsa na siyasa yake da muhimmanci fiye da ta jinin al’ummar Jihar Edo.

Ya ce “kiyaye martabar Zaben Gwamnan Jihar Edo daga duk wani nau’i na rikici ko tayar da zaune tsaye, nauyi ne da ya rataya a kan dukkanin al’ummar jihar.

“Saboda haka dole ne dukkanin masu kishin ganin dorewar dimokuradiyya da wanzuwar ‘yancin, su jajirce wajen tantance shugabanni na gari da za su wakilce su a gwamnati”, inji shi.

Ya nemi jam’iyyar PDP wadda ke riko da akalar jagoranci a jihar da ta tabbatar ta kiyaye doka, da tsarin dimokuradiya gami da akidu na kundin tsarin mulki domin tabbatar da zaben cikin lumana.