✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta dakatar da Giadom a Ribas

Jam’iyyar APC, reshen Jihar Ribas ta dakatar da Honorabul Victor Giadom bisa abin da ta kira yin karan tsaye ga kundin tsarin jam’iyyar. A takaddar…

Jam’iyyar APC, reshen Jihar Ribas ta dakatar da Honorabul Victor Giadom bisa abin da ta kira yin karan tsaye ga kundin tsarin jam’iyyar.

A takaddar da Mai Magana da Yawun sabon Shugaban Jam’iyyar na Ribas Livingtone Wechie ya raba wa ‘yan jarida, ya ce an dakatar da Giadom daga duk wasu ayyukan jam’iyyar saboda karya dokokin jam’iyyar da ya yi da suka bata mata suna da kima.

Hakanan kuma suka yi kira ga Victor Giadom da ya rubuta takaddar ban hakuri ga jam’iyya ya kuma wallafa a jaridu uku.

Takardar ta kara da cewar matakin kwamitin da aka gabatar ya samu karbuwa kuma shi ne matsayin shugabannin Jam’iyyar APC a jihas Ribas.