✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta bukaci Saraki da Dogara da su yi murabus

Jam’iyyar APC ta shawarci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogaro da su yi murabus daga mukamansu. APC ta ce,…

Jam’iyyar APC ta shawarci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogaro da su yi murabus daga mukamansu.

APC ta ce, masu rike da mukaman biyu su ajiye mukamansu don majalisar ta ci gaba da ayyukan da ke gabanta, da kuma wakiltar jama’ar da suka zabe su.

Mukaddashshin sakataren jam’iyyar APC na kasa Mista Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan jiya Lahadi a Abuja, yayin da yake martani akan gangamin da wasu shugabannin jam’iyyar PDP suka yi a Abuja makon jiya.