Tun da jam’iyyun siyasa a Najeriya suka fara shirye-shiryen gudanar da zabukan fid-da-gwani aka fara samun matsaloli da suka shafi ’ya’yan jam’iyyun har kuma zuwa lokacin da aka kammala zabukan na fid-da-gwani wanda da yawa suka bar baya da kura.
Manyan jam’iyyun siyasa a kasar kamar APC da PDP na ci gaba da samun matsaloli da ke yi musu barazana musamman duba da yadda babban zaben 2023 ke kara karatowa.
Aminiya ta yi duba tare da dauraya game da halin da Jam’iyyar APC a Jihar Kano ke ciki, wanda bisa ga dukkan alamu idan ba ta yi da gaske ba, za ta iya yin kitso da kwarkwata a zaben da ake shirin shiga a watan Fabrairun 2023.
Rikice-rikicen shugabanci a jam’iyyar
Jam’iyyar a baya-bayan nan ta sha fama da rikice-rikicen da suka shafi shugabanci a jihar, lamarin da ya kai ga tsagi biyu gudanar da zaben neman takarar shugabancinta a jihar.
A wancan lokaci, gwamann jihar, Abdullahi Umar Ganduje da tsaginsa sun gudanar da zabe tare da zabar Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar, yayin da shi kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau da jama’arsa suka zabi Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar.
Wannan takaddama ta kai su ga jifan juna da munanan kalamai, inda ta kai jam’iyyar na shirya tarukan siyasa amma ba ta kiran tsagin Shekarau duk da cewa suna matsayin ’ya’yan jam’iyyar.
Daga karshe dai kotu ce ta raba gardama inda ta ayyana Abdullahi Abbas, daga tsagin gwamnan jihar, a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar.
Sauya shekar Shekarau da Sha’aban Sharada
Lamarin da ta kai ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ficewa daga jam’iyyar zuwa Jam’iyyar NNPP tasu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Hakazalika, wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar kamar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Birni, Sha’aban Ibrahim Sharada da mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Kafofin Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad, duk sun koka lokacin da suka shiga zaben fidda-gwanin jam’iyyar, inda suka ce tsagin gwamnatin jihar ya yi karfa-karfa wajen bai wa wadanda suke so takara tare da hana damar gudanar da sahihin zabe.
Wannan lamari ya sanya Sha’aban Ibrahim Sharada ficewa daga APC zuwa Jam’iyyar ADC, inda zai yi takarar kujerar gwamnan jihar.
Tun bayan da gwamna Ganduje ya raba gari da uban gidansa a siyasa (Kwankwaso), ya shiga nemo dukkanin wasu mutane da ke da matsala da uban gidan nasa; ya ja su suka yi tafiya tare duk da cewa kowanennsu na da bambancin ra’ayin siyasa.
Matsaloli masu kama da irin wannan sun taru sun yi wa jam’iyyar a APC a Kano katutu.
Ganduje ya yi kokarin dinke jam’iyyar
Tun bayan da jam’iyyar ta tsayar da mataimakin gwamna jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa, ake dambarwa a kan lamarin.
An jiyo Murtala Sule Garo yana korafi kan cewa shi ne wanda ya fi cancantar Ganduje ya bai wa tikitin takarar gwamnan jihar, duba da irin gudummawar da ya bayar a zaben 2019, wanda ya kai jam’iyyar ga nasara.
Ire-iren wadannan matsaloli suka sa Ganduje ya janye muradinsa na tsayawa takarar Sanatan Kano ta Arewa, inda ya bar Sanata Barau I. Jibrin kujerarsa don ya sake yin takara, tun da jam’iyyar ba ta ba shi damar neman kujerar gwamnan jihar da yake muradin zama ba.
Haka kuma, gwamnan ya dinga jele yana mari wajen bin Murtala Sule Garo da ma ire-irensa yana ba su hakuri tare da dannar kirji kan ganin sun hakura an yi tafiya tare.
Duk da wancan kokari na Ganduje sai kuma wata sabuwar baraka ta sake kunno kai tsakanin dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar, Murtala Sule Garo da kuma Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan zargin ana mayar da wasu saniyar ware a jam’iyyar.
Sabon rikici ya kunno kai
Wannan sabon rikici ya yi sanadin fasa wa Garo baki kamar yadda ya bayyana da bakinsa sakamakon wata hatsaniya da ta kaure a tsakaninsu a gidan dan takarar gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna.
Idan ba a manta ba Jihar Kano ce ta bai wa Jam’iyyar APC kuri’u mafi rinjaye a zabukan 2015 da kuma 2019 a fadin Najeriya.
Sai dai wannan rashin zaman lafiya na iya yi wa mata illa a zaben 2023 da ke kara karatowa.
Abun kunya ne shugabannin al’umma su yi fada
Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami ne kuma mai yin fashin baki kan al’amuran siyasa, ya bayyana ra’ayinsa kan rigingimun cikin gida da APC ke fuskanta da irin tasirin da zai iya haifar mata a zaben 2023.
“Wannan abu da ya faru a tsakaninsu ba yanzu ya fara ba, yana da dan tsawon tarihi a tafiyarsu ta siyasa a nan Kano.
“Na farko dai abun kunya ne a ce shugabannin jama’a har sun kai ga fada, za a iya samin bambancin ra’ayin siyasa wanda shi ne dama siyasa ta gada, amma har ta kai ga fada gaskiya wannan dai abin kunya ne ga shugabannin jama’a.
“Sannan na biyu, irin wannan abun ne wanda zai iya tasiri a kan tafiyarsu ta siyasa.
“Abin da zai faru shi ne kowane zai samu kalubale idan zai shiga filin zabe ne kansa a rarrabe, wato yana rigimar cikin gida kuma yana takarar da wasu.
“Abu na uku, shi ne idan aka duba tarihi a siyasar Najeriya, yawancin za ka ga kowa na kokarin ganin sai ya kai dan uwansa kasa ne a zabe kamar yadda ya faru lokacin da aka samu rarrabuwar kai a jam’iyyar CPC wadda ta dinga yakar kanta da kanta, har ya kai ta ga faduwa a zabe na kasa da kuma a jihohi daban-daban.
“Haka nan, idan aka duba can baya, lokacin da aka yi gurguwar Jamhuriya ta uku a nan Kano, irin wadannan rigingimu na cikin gida ya sa Jam’iyyar PDP ta fadi a wurare da yawa.
“Abu na hudu, shi ne irin wannan yakan kawo tashe-tashen hankali a wurare daban-daban, wanda shi ma idan muka duba tarihi kamar irin rigingimu na cikin jam’iyya kamar AG a Jamhuriya ta farko shi ya kai ga tashe-tashen hankali da kashe-kashe da kone-kone wanda ya bai wa soja fuskar su kau da tsarin dimokuradiyya.
Jam’iyya mai rauni ba a samun rigingimu —Doguwa
Da Aminiya ta tuntubi wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, kan wannan dambarwa, ya kada baki ya ce “Ai babu wata rigima da za a ce tsakanin bangarori a Jam’iyyar APC a Kano.
“Gaskiya ne cewa an samu takaddama ko kuma rashin fahimta tsakanin shugabannin guda biyu a nan Jihar Kano, amma wannan abin da ya faru abubuwa ne da za mu ce na cikin gida kuma a cikin tsari na tafiyar da jam’iyya da tsari na tafiyar da gwamnati dole ne za ka samu ’yan rigingimu.
“A cikin gidanka ma dole ne ka samu ’ya’yan da ka haifa ba za su rasa samun bambanci ko kuma ’yar takaddama ga junansu ba, don ya faru aka samu wata gaba sai wadansu su yi amfani da ita don su cimma irin nasu burin.”
Duba da ganin zaben 2023 na kara karatowa, ya yi karin haske kan irin halin da jam’iyyar za ta ita tsintar kanta a ciki.
“Ai wannan shi ne cikar ita kanta Jam’iyyar APC a Jihar Kano.
“Jam’iyyar da ba ka jin labarinta ai ba ka jin irin wadannan ’yan rigingimun na tasowa.
“Saboda haka ita jam’iyya za ta kai bantenta ne idan aka samu irin wadannan ’yan rigingimu.
“Duk jam’iyyar da ba ka ji ana samun wannan ba, to ba ta da ma mutanen da za su yi rigima.
“Amma idan ka dubi yadda Jam’iyyar APC take a cikin Jihar Kano da irin mutanen da take da su da irin abubuwan da ta sa a gaba, ai dole irin wadannan abubuwan su taso kuma tana da wadansu hanyoyi da take maganin rigingimu idan sun taso.
“Saboda haka ina so na tabbatar maka ko wadannan rigingimun da ake magana tsakanin shi Alhassan Ado Doguwa da shi dan takarar mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo, abu ne wanda iyayen jam’iyya za su iya maganinsa kuma in sha Allahu nan da dan kankanin lokaci za ka ga an yi maganinsa,” in ji shi.
Ana kokarin sasanta bangarorin
Shi kuwa sakataren jam’iyyar APC na Jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina, cewa ya yi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kokarin ganin sun daidaita bangarorin biyu da suka samu matsala kuma za su tattauna da manema labarai amma ba a wannan lokacin ba.
Rigimar ba za ta amfani kowa ba
Farfesa Sani Fage ya ce, “Wannan rigimar abu ne da ba zai haifar wa kowa da mai ido ba,” cewar Farfesa Fagge.
Sannan ya ce ire-iren wadannan rigingimun na cikin gida na iya shafar duka zabukan jam’iyyar tun daga jihar har zuwa matakin tarayya.
“Zai shafi kasa mana, saboda abu ne na zabe kuma idan jam’iyya ta rasa yadda aka tsaro tsarin zabe, zai iya yiwuwa ita uwar jam’iyyar illa a zabe gaba daya.
“Misali daya daga cikin abin da aka bayar, jam’iyya ta kafa shugaban kasa shi ne ta ci kuri’u mafiya rinjaye sannan kuma ta ci daya bisa ukun kuri’u na jihohi akalla 24, to idan ana samun irin wannan ko da a jiha daya ne aka samu irin wannan za a iya gurgunta ka’ida ta zabe.
“Sannan kuma Kano jiha ce mai kuri’u da yawa don haka idan jam’iyya ta fadi Kano zai yi wuya misali a ce ta samu kuri’un da zai kai ta samu nasara a wancan mataki.
“Sannan kuma a Arewa da ma Najeriya wata alkibla ce ta siyasa, tashe-tashen hankali a Kano zai iya faruwa a sama ko a wasu wurare wanda duk zai iya sa duk jam’iyyar ta yi asara ba wai kawai zaben jiha ba har na kasa ma baki daya.”
Sai dai ko ma mene ne, jam’iyyar a matsayinta Na mai mulkin jihar, akwai bukatar shugabanninta su yi karatun ta nutsu don ganin sun tsallake siradin zaben 2023, ko kuma za a iya ta maganar Malam Bahaushe, wato za a yi ‘da kwance, uwa kwance.’