✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC bakarariya ce ba ta haihuwa — Sule Lamido

APC ta haifa ’yan uku, inda ta kyankashe gwamnonin PDP guda uku.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce, Jam’iyyar APC mai mulki bakarariya ce da ba za ta iya daukar ciki, ballantana ta haifi dan kirki a batun shugabanci nagari.

Sule Lamido wanda kuma jigo ne a Jam’iyyar PDP, ya ce taron kasa da PDP ta gudanar na mutanen kasa ne ba na jam’iyyarsu ba.

Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a hedikwatar Kamfanin Media Trust da ke Abuja a ranar Talata da ta gabata.

Ya ce an kafa APC ce kawai domin ta karbi mulki, amma ba ta da tsari da kwarewar da ake bukata don tafiyar da mulkin.

Ya ce, “A kullum cewa suke yi ba mu iya ba. Suna cewa PDP kazanta ce, amma kuma kullum suna bibbiyar mambobinmu suna so su koma jam’iyyarsu.

“Babu wani wanda asalinsa APC ne a cikinsu. Jam’iyya ce mai cike da rashawa.”

Game da Babban Taron PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce, “Taron da muka gudanar ba na PDP ba ne kawai, taro ne na Najeriya lura da yanayin rashin tsaro da ake ciki da rabuwar kai da kuma tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke ciki a yau.

’Yan Najeriya suna bukatar canji.”

Alhaji Lamido ya kara da cewa Jam’iyyar PDP ta jama’a ce tun a farko, inda ya ce tun asali an kafa ta ce domin dawo da martabar kasar nan.

“Bayan tataburzar da aka yi na 12 ga Yuni, sai kasar ta fada cikin rudu da rashin aminci.

Haka ma lokacin da Abacha ya fara mulki. Hakan ya sa muka yi tunanin muna bukatar dimokuradiyya ta gaskiya da za ta hada kasar baki daya, sannan ta dawo da kaunar juna.

“Lokacin da Abacha ya fara tunanin zarcewa, sai muka ce ba zai yiwu ba. Nan ne muka kafa G9; da ni da marigayi Bola Ige da marigayi Solomon Lar da marigayi Adamu Ciroma da sauransu.

Muka ce ba zai yiwu ba a zauna lafiya sai an gyara kuskuren da aka yi na 12 ga Yuni. Nan muka yaki tazarcen Abacha.

Daga nan muka koma G18 muka rubuta wasika zuwa ga Abacha, inda muka kalubalanci tazarcen da yake shirin yi.

Solomon Lar ya ce tunda shi ne babba a cikinmu, shi zai kai wasikar “Koda an kama ni, sai ku boye.

A daren ranar aka zo aka kami ni da Rimi, ba a sake mu ba sai bayan da Abacha ya rasu,” inji shi.

Ya ce daga nan suka zauna suka yi tunanin kafa jam’iyyar da za ta hada kan kasar nan, inda da hakan ne suka kafa PDP.

Alhaji Lamido ya ce nan ne iyayen jam’iyyar suka amince a tsayar da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo daga yankin Yarbawa maimakon Alex Ekwueme domin suna so samar da zaman lafiya da aminci a tsakanin ’yan kasar nan bayan rashim yarda da aka samu a kan zaben 12 ga Yuni.

Da wakilinmu ya tambaye shi batun tsayar da dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar, sai ya ce ba wai bangaranci ne abin lura ba, ya ce burinsu shi ne su fitar da mutanen Najeriya daga kangin da suke ciki na tashin hankali da rashin tsaro.

Mun haifi ’yan uku — APC

A martanin Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC ta Kasa, Yekini Nabena kan kalaman Lamido ya ce, “Za mu bar PDP su yi surutunsu, mu kuma muna aikinmu a karkashin kasa.

APC ta haifa ’yan uku, inda ta kyankashe gwamnonin PDP guda uku, kuma har yanzu tana da ciki kuma za mu kara haifan wasu ’yan ukun.”