✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ba ta shirya wa mulkin kasar nan ba – Shehu Gabom

Alhaji Shehu Musa Gabom tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi kuma jigo a Jam’iyyar PDP ta kasa, a tattaunawa da wakilinmu ya ce bai…

Alhaji Shehu Musa Gabom tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi kuma jigo a Jam’iyyar PDP ta kasa, a tattaunawa da wakilinmu ya ce bai kamata a fara adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari a yanzu ba, inda ya ce an ci da zucci wajen yin haka:

Aminiya: Yaya kake ganin tafiyar sabuwar gwamnatin Muhammad Buhari?
Shehu Gabom: Tun lokacin da aka zabi Muhammadu Buhari, abin da na fada shi ne siyasa ta riga ta wuce, domin an yi yakin neman zabe kuma an zabi Buhari a matsayin Shugaban kasa, don haka abin da ya dace shi ne a hada kai a mara masa baya don ya ciyar da kasar gaba. Domin idan ka ce ma za ka yi adawa tun yanzu, a kan me za ka yi adawar? Tunda babu wani abu da ya yi da za ka yi adawar a kansa. Kuma ai adawa ana yin ta ne idan aka yi wasu kura-kurai ko wasu abubuwan da ba su dace ba. Kuma babu gwamnatin da za a yi wadda ba za a samu kura-kurai ba. Saboda haka mu da muke jam’iyyar adawa ta PDP, yanzu muna kallon yadda abubuwa suke tafiya da idon basira ne, kuma inda muke ganin za mu iya jawo hankali a yi gyara sai mu jawo a yi gyaran. Bai kamata a yi adawar hauka ba, ana adawar ilimi ne kuma ana yin adawa ne don a gyara kasa. Saboda haka dole ne mu yi hakuri mu san cewa kasar nan ta shiga wani hali mai wahala. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi kasar nan a cikin wani mawuyacin hali, don haka dole ne ya tafiyar da kasar a hankali. Domin duk kasar da ka zo ka karba wadda barna ta yi yawa a cikinta kuma ka ce da garaje za ka yi gyara, gyaran ba zai yiwu ba.
Aminiya: To, amma wasu daga cikin jami’an jam’iyyarku ta PDP suna ta sukar gwamnatin ta Buhari kan tana tafiyar hawainiya a mulkinta me za ka ce?
Shehu Gabom: Kowane Shugaban kasa akwai yadda yake tafiyar da gwamnatinsa. Wani yana da gaggawa a cikin mulkinsa wani yana yi a hankali da natsuwa. Don haka har yanzu muna karantar yadda yake gudanar da mulkinsa. Yanzu wajen wata biyu ke nan da kama mulkinsa, har yanzu bai yi komai ba a kasar, ban da nada mataimakansa na ’yan siyasa da canja shugabannin tsaro. Amma har yanzu bai nada ministoci ba, bai nada mataimakansa na ofis da sauransu ba. Yawaicin abubuwan shi ne yake yi, shi kadai. Shi ya sa nace ana karantar abu kafin ka ce za ka fara magana a kai.
Saboda haka idan ka yi gaggawar nuna adawa don kana dan adawa ka yi garaje. Ni a ra’ayina haka nake gani, ba ina magana a madadin jam’iyyata ba ne. Muna kallon yanayin yadda yake gudanar da mulkinsa, kuma muna bi sannu a hankali. Domin a yadda ya karbi kasar nan, kamar yadda na fada kowace jam’iyya kake ka san an karbi kasar nan a cikin wani mummunan yanayi mai wahala. Saboda haka shi ya san abin da ya tarar a wurin, duk wanda yake waje bai sani ba. Don haka a ba shi lokaci ya zauna ya kafa gwamnatinsa a ga yaya zai gudanar da gwamnatin tasa. Wadannan su ne abubuwan da ya kamata a yi
la’akari da su, kada a yi gaggawar hura wuta a kasar, domin kasar nan tana cikin zafin sosai. Don haka dole ne a bi kasar a hankali don a gyara ta a samu zaman lafiya.
Aminiya: To, me za ka ce game da yunkurin da jam’iyyarku ta PDP take yi na ganin ta sake dinke kanta don tunkarar zaben shekarar 2019?
Shehu Gabom: Ai dole ne Jam’iyyar PDP ta sake dinke kanta don tunkarar zabe na gaba. Kuma kuskure da rashin iya shugabanci ne ya sa Jam’iyyar PDP ta fadi a zaben da ya gabata. Domin ba ’yan siyasa ba ne aka sa a shugabancin jam’iyyar, yawaicin shugabannin jam’iyyar ’yan kwangila ne aka dauki shugabancin jam’iyyar aka ba su. Kuma babu mai iya shugabancin jam’iyya sai dan siyasa. Ba za ka dauko mutumin da ya yi soja ko ya yi aikin dan sanda ya yi ritaya ko kuma wanda harkokinsa na kasuwanci kawai yake yi, ka ce za ka ba shi shugabancin jam’iyya ba.
Shugabancin jam’iyya sai dan siyasa wanda yake zuwa karkara ya san halin da mutane suke ciki yake magana da su. Yawaicin wadanda suka shugabanci Jam’iyyar PDP a matakin kasa idan ka dubi tarihinta in ka cire marigayi Cif Solomon Lar da Cif Audu Agbe da Cif Gemade duk sauran shugabannin da aka yi ba ’yan siyasa ba ne. Mutane ne wadanda aka yi alfarma aka dora su kan kujerar shugabancin jam’iyyar. Shi ya sa aka samu matsala a cikin jam’iyyar wadda ta kai ta ga faduwa.
Aminiya: To, kana ganin idan jam’iyyar taku ta dinke za ku cimma nasara a zaben shekara ta 2019?
Shehu Gabom: Ai da yardar Allah babu abin da zai hana Jam’iyyar PDP sake karbar mulki a zaben shekara ta 2019. Domin wadanda suka karbi mulkin a yanzu an ga yadda suke tafiya. Kowane mutum ya san duk jam’iyyar da ta yi shekara 16 a kan mulkin kasar nan dole ne wannan jam’iyya ta samu gugewa.
Saboda haka babu wata jam’iyya da ta kai Jam’iyyar PDP sanin kasar nan, kuma babu wata jam’iyya da ta kai ta yawa magoya baya a Najeriya. kuma babu wata jam’iyya da ta kai ta kafuwa tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi a Najeriya.
Kamar yadda na ce ne abubuwa da yawa ne suka kawo faduwar PDP, kamar rashin amana da rashin sanin darajar dan Adam wadannan su ne suka tursasa mutane suka yi mata bore a zaben da ya gabata. Don haka idan aka samu shugaba na kwarai a Jam’iyyar PDP wanda ya san martabar jama’a ya san yadda ake tafiyar da shugabancin jam’iyya a cikin wata biyu mutuncin wannan jam’iyya zai dawo.
Aminiya: Yaya kake ganin tafiyar Jam’iyyar APC a yanzu?
Shehu Gabom: Bisa dukkan alamu Jam’iyyar APC sun nuna cewa ba su san yadda ake gudanar da mulki ba. Mu a Jam’iyyar PDP mun saba da rigingimu iri-iri wannan rigima ta taso mu kashe wancan ta taso mu gyara wannan ta taso mu sasanta. Su a Jam’iyyar APC ba su saba da irin wadannan rigingimu ba, domin ba su san mulki ba ba su san yadda ake tafiyar da shi ba. Sun zo sun karbi mulkin kasar nan amma ba su shirya yadda za su tafiyar da mulkin ba. Don haka ina tausaya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shi ne yake tsaka-mai-wuya. Domin shi kadai ne wanda yake tunanin yaya kasar za ta yi ta ci gaba. Amma yawancin ’yan jam’iyyar ta APC ba su da ra’ayin kasar ta ci gaba sai dai ra’ayin son zuciyarsu kawai.
Aminiya: Yaya kake kallon rikicin shugabancin da ake yi a Majalisar Dokoki ta Tarayya a yanzu?
Shehu Gabom: Duk wannan rikici na majalisun biyu na tarayya shi ma rashin iya shugabanci ne. Domin kai shugaban bai kamata ka ce ba ka damu da abin da yake faruwa a majalisa ba. Domin majalisar nan ita ce za ta tabbatar da abin da shugaban yake son ya gudanar a kasar nan.
Kamar maganar yaki da cin hanci da rashawa da Shugaban kasa yake magana ba zai yiwu ba, sai da majalisa, domin su ne suke yin dokar. Don haka ba zai iya gudanar da wannan shiri ba, dole sai da
majalisa. Kuma kashi 70 cikin 100 na cin hanci da rashawa, ma’aikatan gwamnati ne, kuma ma’aikatan gwamnatin na tarayya ne. Don haka idan ya yaki cin hanci da rashawa a cikin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya za a ce an shawo kan matsalar cin hanci da karbar rashawa a Najeriya.
Domin idan ka ba mutum minista wadannan manyan ma’aikatan gwamnati su ne suke bata duk wani sabon minista da aka kawo, su ne suke nuna musu hanyar da za a yi cuta. Don haka dole ne Shugaban kasa zai hada kai da bangaren ’yan majalisa da bangaren shari’a a wannan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Aminiya: A karshe wace kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?
Shehu Gabom: Kira na ga al’ummar Najeriya shi ne mu ci gaba da yin addu’a ga kasar nan. Domin kasar nan tana cikin wani mummunan hali na yaki da ’yan Boko Haram. Shugaban kasa yana bukatar hadin kan kowa kan wannan yaki don a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.