A daidai lokacin da al’umma suka fara hangen matsalolin da suka dabaibaye Najeriya sun zo karshe, shi ne, lokacin da jam’iyyun adawa suka dunkule wuri daya a matsayin jam’iyya daya mai karfi (mega party), domin su fitar da al’ummar Najeriya daga cikin halin da suke a wancen lokacin. Tabbas hakan ya yi tasiri, domin an samu abin da ake nema, wato canjin Gwamnati, musamman a matakin shugabancin kasa da sauran wasu jihohi a Arewacin Najeriya. Hakika duk wannan nasarorin da jam’iyyar APC, tare da goyan bayan al’ummar Najeriya ta samu ya ta’allaka ne akan kyakkyawan tsari da kyakkyawan shugabanci da take da shi a matakin uwar jam’iyya ta kasa, har zuwa matakin kananan hukumomi.
Shugabanci ba ya tabbata sai an samu sahihan shugabanni, masu gaskiya da rikon amana; kuma suka gina jam’iyyar akan turba mai kyau, sannan suka tsaida nagartattun mutane a matsayin wakilai.
Don haka ina kira ga sabon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina Alhaji Shitu S. Shitu (masalaha) da cewa; adalci shi ne isar mulki. Kuma tabbas akwai babban kalubale akansa na zakulo mana sahihan mutane a matsayin ’yan takara, tun daga matakin Gwamna, ’yan majalissu jiha da na tarayya da sauran matakan kananan hukumomi. Daga karshe ina addu’ar Allah ya tashi riko, kuma ya ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa na jam’iyya da ma al’umma baki daya.
Adamu Aliyu Amo, Katsina, Sakataren kungiyar Muryar Jama’a reshen Jihar Katsina. 09097300909 [email protected]
APC a tabbatar da adalci a Katsina
A daidai lokacin da al’umma suka fara hangen matsalolin da suka dabaibaye Najeriya sun zo karshe, shi ne, lokacin da jam’iyyun adawa suka dunkule wuri…