✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Annoba ce ta hana mu yi wa marayu kayan sallah’

Sallar bana ta sami jama’a da dama cikin mawuyacin yanayi, sakamakon kasancewar annobar coronavirus da ta addabi duniya dama irin matakan kariya da mahukunta suka…

Sallar bana ta sami jama’a da dama cikin mawuyacin yanayi, sakamakon kasancewar annobar coronavirus da ta addabi duniya dama irin matakan kariya da mahukunta suka dauka domin kare yaduwar annobar.

Lamarin da ya yiwa tattalin arzikin kasa da na daidaikun jama’a illar gaske.

Hakan ne ya sanya a lokacin sallar Idi karama jama’a da dama basu sami damar gudanar da abubuwan da suka saba yi a lokutan bikin sallar a baya.

Alhaji Umar Lawal Atana, shugaban kwamitin da ke kula da marayu a jihar Legas da ke karkashin kungiyar Izalatil Bidi’a wa ika’amatis Sunnah ya shaida wa Aminiya cewa a sallar bana basu sami ikon yiwa maryun su dinkin  salla ba, kamar yadda suka saba yi a baya.

Yace annobar coronavirus ne ta yanke masu hanzari, ” har mun fara shirya-shiryen fara aikin yiwa marayun kayan salla, domin muna da rijistar yara marayu sama da 4000 a Legas, kuma a duk shekara muna yi masu kayan sallah mazan su da matansu tun daga kan hula, da riga da wado da takalmin sallah, su kuma mata da hijabi, muna kuma kula da lafiyar su,

“Ingantattun kayan sallah muke dinka masu ta yadda ba za ka iya gane cewa marayu ba ne idan sun hadu da sauran yara, a bana mun fara aiki sai aka fara wanna annoba, kuma aka rufe wuraren Ibadu aka kuma kulle ko ina aka hana mutane walwalar kasuwanci da al’amuransu na yau da gobe, wannan ne yasa muma dolle muka dakata da aiki.

“Daman wuraren da muke neman taimakon kudin, mafi akasari a masallatai ne a lokacin tafsirin azumin Ramadan, da kuma kasuwanni da wuraren wa’azi, kuma duk wadannan a hanasu an rufe masallatai da kasuwanni da bankuna, sai ya zamana babu inda zamu je mu nema wa marayun taimako.

” Sai daidaikun jama’a da suka saba bada gudunmawa sune suka waiwaye mu, sai muka yi amfani da dan abin da muka tara muka sayi kayan abinci da magani, domin a wannan lokacin marayun namu mun lura sun fi bukatar abinci da magani duba da halin kulle da ake ciki iyayensu mata basu da zarafin kulawa dasu.

“A daidai lokacin da sallah ta matso iyayen yara sun yi ta zuwa su na tambayar kayan sallar yaran, amma mun yi ta basu hakuri, bamu ji dadin haka ba, suma basu ji dadi ba, haka ma yaran, kasan shi yaro abin da ya saba ana yi masa in lokacin yayi sai ya tambaya.

“A shekarun baya mukan tara kudi sama da naira miliyan hudu domin kula da marayun, masu yi mana aikin dinkin kayan suma marayu ne da suka kai munzalin girma da muke basu aiki domin su sami abin dogaro, kasancewar muna yiwa marayun yara ‘yan kasa da shekaru 15 ne kayan sallah, wadanda suka yi hankali kuma muna koya masu sana’ar dogaro da kai ne.

” mu ke daukar dawainiyar karatun su na Islamiya, lafiyarsu da sauran abun da ba a rasa ba” in ji Umar Atana.

Yace a bana sun baiwa yaran hakuri saboda rashin kayan sallah, suna fatan in Allah ya yarda za su yi masu a shekara mai zuwa.