A ranar Litinin da ta wuce ce kafar watsa labarai ta Naija News ta ruwaito cewa kulob din Everton da ke Ingila ya dauki Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocinsa.
Idan za a tuna kulob din Everton ya kori tsohon kocinsa ne dan asalin Portugal, Marco Silba a kwanakin baya saboda rashin kokari.
Ancelotti wanda ya samu nasara a harkar horarwa, ya lashe manyan kofuna 20 a kulob daban-daban ciki har da na gasar Zakarun Turai sau uku.
Ya taba horarwa a kulob da dama da suka hada da Chelsea na Ingila da Inter Milan na Italiya da Bayern Munich na Jamus da Real Madrid na Spain da sauransu.
A wata hira da aka yi da sabon kocin ya nuna farin ciki game da damar da mahukntan kulob din suka ba shi don horar da kulob din, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin wadanda suke da kwarasrrun ’yan kwallo. Ya sha alwashin farfado da martabar kulob din a idon duniya a matsayinsa na sabon koci.