✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zullumi kan rufe asibitin yara a Kano

Kamfanin da ke kula da asibitin yara na titin Gidan Zoo na kwashe kayansa.

Marasa lafiya a asibitin yara da ke titin Gidan Zoo a birnin Kano sun shiga cikin fargaba cewa Gwamnatin Jihar Kano ta rufe asibitin.

Batun rufe asibitin, shekara uku bayan fara aikinsa, ya jefa likitoci da ma’aikatan jinya cikin rashin tabbas game da makomarsu, yake kuma cikas ga sha’anin kula da marasa lafiya.

Ma’aikatan asibitin sun tabbatar da samu umarnin kotu na kwashe kafatanin kayan aiki da ma’aikatan kamfanin Northfield Health Services da ke kula da asibitin, saboda wani sabani tsakankin shugabannin asibitin.

Marasa lafiya sun shiga tsaka mai wuya tare da fargabar halin da za su tsinci kansu idan likitoci da ma’aikatan suka dauke kafa.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa marasa lafiya sun fara dauke kafa a asibitin da a baya daruruwan mutane ke zuwa domin samun kulawa.

Wani daga cikin shugabannin ma’aikatan asibitin ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa, “Ba mu san makomarmu ba, saboda babu wani bayani da akai mana, wadanda ke kula da asibiti da shugabannin asibitin ne suka samu sabani, don haka sai an warware matsalar”.

Amma a zantawarsu, Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar a Kano, Dokta Nasiru Kabo, ya ce ba ta rufe asibitin gwamatin jihar ta yi ba.

Amma ya ce Gwamnatin Jihar Kano ta warware yarjejeniyar kawancen aiki  tsakaninta da Northfield Health Services saboda rashin gamsuwa da yadda kamfanin yake kula da asibitin.

Sai dai bai dai yi karin haske game da umarnin kotun da kuma makomar asibitin ba.