✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin tsofaffin ’yan sanda biyu da kisan ’yar siyasa a Brazil

An kama wasu tsofaffin jami’an ’yan sanda biyu a kasar Brazil, inda ake zarginsu da hannu wajen kisan wata ’yar siyasa mai suna Marielle Franco,…

An kama wasu tsofaffin jami’an ’yan sanda biyu a kasar Brazil, inda ake zarginsu da hannu wajen kisan wata ’yar siyasa mai suna Marielle Franco, wadda Kansila ce bakar fata mai yawan magana a majalisa a babban birnin kasar na Rio de Janeiro.

Shekara daya ke nan da kisan ’yar siyasar da direbanta, al’amarin da ya haifar da babbar zanga-zanga a kasar.

Ita dai Mis Franco ta kasance mai yawan sukar yadda aka rika jibge jami’ar tsaro na Gwamnatin Tarayya garuruwan da ke makwabtaka da birnin na Rio, inda talakawa ne marasa galihu suka fi zama a cikinsu.

Mutanen biyu da aka kama dai, sun kasance jami’an ’yan sanda da suka yi ritaya daga aiki.

A bara ne dai, ranar 14 ga watan Maris aka kashe ’yar siyasa Franco, a lokacin da take dawowa daga wani taro da aka shirya da nufin tallafa wa mata bakaken fata, a yayin da wata mota ta zo daidai saitin tata motar, inda aka bude mata wuta da bindigogi har sau tara, inda a sakamakon haka ita da direbanta suka rasa rayukansu.