Tashin hankali ya sake kunno kai a Masarautar Kano, inda aka zargi wasu magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da kutsawa cikin fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta Gidan Rumfa da ke Kofar Kudu.
Shaidu sun bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne lokacin da tawagar Sarki Aminu ke dawowa daga gaisuwar rasuwar attajirin ɗan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
- Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina
- HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya
A wata sanarwa da kakakin masarautar Kano, Sadam Yakasai, ya fitar ya bayyana cewa Sarki Sanusi ba ya cikin fadar lokacin da abin ya faru ba.
“Sun fasa kofar shiga fadar, sun kai wa masu gadi hari, har suka raunata wasu.
“Haka kuma sun lalata motocin ‘yan sanda da ke wajen fadar. Aminu ya yi amfani da titin gidan Sarki maimakon ya bi hanyar Koki zuwa Nasarawa, inda yake zaune. Wannan ya nuna cewa da gangan ya nufi Gidan Rumfa.”
Yakasai, ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko da Sarki Aminu ke fakewa da hanyar Gidan Rumfa ba, yana jefa fargaba a zukatan mazauna unguwar.
Wani makusancin Sarki Sanusi, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin ya faru ne da gozon bayan wasu daga cikin majalisar Sarki Aminu.
Ya ce wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta kafin tashin hankalin ya tabbatar da hakan, inda aka jiyo wani daga cikin majalisar yana tabbatar da abin da za su yi.
Tawagar Sarki Bayero ta musanta
Sai dai wani daga cikin tawagar Sarki Aminu Ado Bayero, Mukhtar Dahiru, ya ƙaryata zargin.
Ya ce: “Ni kaina ina cikin tawagar Sarki Aminu a lokacin. Mun dawo daga Koki ne bayan gaisuwar rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata. Sai dai a kusa da fadar Ƙofar Kudu muka tarar da wasu ɓata-gari da suka rufe hanya ɗauke da muggan makamai.
“Masoya Sarki ne suka tunkare su domin su ba mu hanya mu wuce.”
Ya ƙara da cewa babu wani hari da suka kai wa jami’an tsaro a fadar Sarki Sanusi, sai dai ‘yan sanda ne suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin shawo kan lamarin.