✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin shugaban makaranta da yin lalata da dalibansa 7 a Kwara

Makarantar ta ce babu dalibanta a cikin sunayen da ake ikirarin an yi wa fyade

Dambarwa ta biyo bayan zargin lalata da dalibai  bakwai da ake yi wa Shugaban Kwalejin Musulunci ta Hassanat  da ke Ilori a Jihar Kwara.

Wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa shugaban mai suna Samuel Prosper ya buya, tare da rokon a yafe masa.

To sai dai binciken Aminiya ya nuna a ranar Alhamis gwamnati ta rufe makarantar, sai dai zanga-zangar shugabbaninta ya sanya Ma’aikatar Ilimi sake bude ta.

Wata ma’aikaciuya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce duk da shugaban da ake zargi ya ajiye aiki, makaranatar ba ta da dalibai masu sunyaen da kafafen yada labarai suka rawaito a makaranatar.

Ta kuma ce sunaye biyu ne kadai na dalban nasu, suma kuma sun karyata labarin.

Ta ce kafin wannan lokacin, shugaban makaranatar ya sha korafin ana yi wa rayuwarsa barazana, musamman kasancewarsa Kirista da ke jagorantar makaranatar Musulmi mai zaman kanta.

“Shi kuma shugaban riko ne, kasancewar tsohuwar shugabar ta samu wani aikin a Abuja.

“Da yake shi ne mataimakinta, sai aka ba shi kafin zabar wani sabon shugaban kuma ana tsaka da haka ne mai makarantar ya rasu,” in ji ta.

Wata makwabciyar makarantar, Misis Mojirayo, ta ce, “Ba mu taba jin wannan labarin ba sai yau da safe.”

Har ila yau, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce babu wani dan jarida da ya tabbatar wa faruwar lamarin.

“Abin da na ce shi ne babu wanda ya shigar da korafi makamncin wannan ofishinmu,” in ji shi.

A nasa bangaren, kakain ma’aikatar ilimi ta jihar, Peter Amongbonjaye, ya ce ba shi da hurumin yin magana kan lamarin.