✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin magidanci da yi wa yaro dan shekara 11 fyade

Wani magidanci mai suna Mohammed Lawal Ahmed ya shiga hannu bayan an kama shi bisa zargin yi wa wani yaro dan shekara 11 fyade. Ana…

Wani magidanci mai suna Mohammed Lawal Ahmed ya shiga hannu bayan an kama shi bisa zargin yi wa wani yaro dan shekara 11 fyade. Ana zargin ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Disamba bayan ya rika ba shi alawa domin yin lalata da shi.

Bayanin kama shi na kunshe ne a cikin wata takardar koke da Hukumar Cibil Defens ta aike wa Kotun Majistrate da ke Kawo, Kaduna, bayan kama wanda ake zargin.

Aminiya ta fahimci cewa mahaifiyar yaron ne ta sa aka kama wanda ake zargin bayan ta ga wasu alamu a jikin yaron a layinsu da ke Titin Ikara a Sabon-Gari a  Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.

Kotu ta ba da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 500, sannan ya kawo ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi  na 15 a  kuma mazaunin Kaduna don tsaya masa. An dage saurarar karar zuwa 16 ga  Janairun nan.

Kwamishinar Mata ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta nuna takaici a kan batun, inda ta ce dole sai an yi wa yaron adalci.

“Wannan abin bakin ciki ne a ce magidanci da mata da ’ya’ya amma a same shi da lalata ’ya’yan wadansu. Batun na gaban kotu inda zai fuskanci hukunci,” inji ta.

Sai ta yi kira ga iyaye su rika kula da ’ya’yansu domin kare su daga fadawa hannun mutanen da za su cutar da su da ake tare da su a wuri guda.