✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin dalibai 5 da kashe abokin karatunsu kan zargin satar waya a Sakkwato

Daliban sun daure Lukman da igiya inda suka yi masa dukan kawo wuka a wani gida.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu dalibai biyar na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Sultan Abdurahman da ke Gwadabawa a Jihar Sakkwato, sun hada baki wajen kashe wani takwaransu mai suna Lukman Malami bisa zargin satar wayar hannu.

Malami, wanda dalibin aikin tiyatar hakori ne a kwalejin, ana zargin abokansa sun kashe shi da safiyar ranar Lahadi bayan da suka bukaci ya mayar musu da wayar da suka yi ikirarin cewa ya sata.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar jami’in kula da harkokin daliban kwalejin, Nafiu Bello, ya ce wadanda ake zargin sun daure Malami da igiya a wani gida da ke wajen harabar kwalejin, inda suka yi masa dukan kawo wuka.

Ya ce daliban sun taru ne a daya daga cikin gidajensu domin murnar fitar da sakamakonsu.

“Sun taru ne don murnar samun sakamakon jarabawa mai kyau, a wannan lokaci ne wayar ta bata kuma Malami na daga cikin wadanda suka fara fita bayan batar wayar wanda hakan ya sa suka zarge shi.

“Bayan ya dawo sai suka ce shi ne ya saci wayar ya je ya boye ta amma ya dage cewa ba shi ba ne,” in ji Mista Bello.

Ya ce daga baya ne daliban suka daure Malami suka fara dukansa har sai da ya suma.

“Sun kai shi asibiti a lokacin da suka fahimci cewa ya fita a hayyacinsa amma kafin su isa ya mutu,” in ji shi.

Mista Bello ya ce daga baya daliban sun dauko gawar daga asibiti amma daga baya ‘yan sanda suka kama su.

“A jiya [Laraba] na kai wasikar korar su ga ‘yan sanda saboda ba za mu iya ci gaba da samun irin wadannan dalibai a cikinmu ba.

“Shugaban makarantar ya jagoranci tawaga don jajantawa iyayen daliban,” in ji shi.

Wani dan uwa ga dalibin da aka kashe, Sanusi Malami, ya ce wadanda ake zargi da kisan sun kawo gawar gidansu ne da safiyar ranar Lahadi.

Ya ce daliban sun shaida wa musu cewa sun tsinci Malami ne cikin jini lokacin da suke komawa gida da safe.

“Mun kai gawar asibiti a nan Sakkwato domin a yi bincike amma sai suka ce sai mun hada da ‘yan sanda. Da ’yan sanda suka zo, sai suka fara yi wa daliban tambayoyi, daga bisani suka tafi da su,” in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar, bai amsa kira da sakon da aka aika masa kan kisan ba.

%d bloggers like this: