✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zanga bayan sake kai hari a Faskari

Al’ummar Karamar Hukumar Faskari na zanga-zanga saboda yadda yankin ya koma tamkar babu tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga. Kwana daya da kai hari a…

Al’ummar Karamar Hukumar Faskari na zanga-zanga saboda yadda yankin ya koma tamkar babu tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Kwana daya da kai hari a garin Kadisau, sai ga shi a safiyar Alhamis mahara sun sake kai wani harin a garin na Faskari.

Hakan ya sa mutanen garin da ma makwabtansu daga yankin ‘Yankara gudananar da zanga-zangar.

Kwana hudu ke nan da yin irin wannan zanga-zangar a garin ‘Yantumaki ta karamar hukumar Dannusa.