A kowane lokaci `yan kasa suna zaman jiran jin jerin cikakkun sunayen irin mutanen da Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari zai mika wa Majalisar Dattawa don neman amincewar ta su kasance Ministocinsa. Bisa ga cika alkawarin da ya yi wa `yan kasar nan tun ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, ranar da ya saba layar kama aiki a zamansa na sabon shugaban kasa na farko daga jam`iyyar APC, jam`iyyar adawa da ta kasance ita ce ta farko da ta fara karbar mulkin gwamnatin tsakiya, a tarihin mulkin farar hular kasar nan da aka fara a shekarar 1960, bayan da kasar nan ta samu `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a wancan lokacin. A lokacin bikin rantsuwar Shugaba Buhari ya fadi cewa, ba zai nada Ministocinsa ba har sai cikin wannan watan na Satumba, kusan watanni hudu ke nan, bayan ya hau kan karagar mulki.
Rashin nada Ministocin har zuwa wannan lokaci ya zama wani abin kace-nace da cece-kuce, musamman daga jam`iyyun adawa, da suke daukar hakan tamfar gazawar gwamnatin ta jam`iyyar APC ne, gazawar da suke ganin ta kawo mummunan cikas da koma baya, cikin gudanar da al`amurran gwamnati na yau da kullum, don ci gaban al`umma da habakar tattalin arzikinsu da na zamantakewarsu da ma duniya baki daya.
Ya yin da ita kuma Jam`iyyar APC da shi kansa shugaban kasa da wasu magoya bayansa, suka dage akan cewa ba abin da ya tsaya cikin tafiyar da al`amurran gwamnatin tsakiyar don ba ta nada Ministoci ba. Shugaba Buhari ya nanata cewa ba wani abin sauricikin nada Ministocin, har ya kan ce yana son ya bi komai daki-daki, domin ya san cewa a cikin gaggawa akwai nadama, wanda shi kuma yana gudun aikin da na sa ni. Bayan gudun yin gaggawa, wani dalilin da za ka iya cewa shi ya sa Shugba Buhari jinkirin nada Ministocinsa, bai rasa nasaba da ba wani sashe na Kundin tsarin mulkin kasar nan da ya tanadi cewa lallai sai shugaban kasa ko gwamnan jiha sun nada Ministoci ko Kwamishinoninsu a cikin wani yankakken lokaci. Ba wai gwamnatin tarayya ba ce kadai zuwa yanzu ba ta nada Ministocinta ba, akwai jihohi 21, da su ma ba su nada Kwamishinoninsu ba zuwa yanzu.
Zuwa yanzu Jaridar banguard, ta ranar Litinin da ta gabata ta ruwaito wata majiya mai tushe ta Jami`an tsaro na farin kaya, wato SSS, da ta tsegunta mata cewa tuni ta fara aiki tantance jerin sunayen wasu daga cikin mutanen da Shugaba Buhari ya tura mata da ya ke son ya nada Ministocinsa, kafin ma ya mika wa Majalisar Dattawa sunayensu don amincewa ta karshe. Wasu daga cikin mutanen da jaridar ta banguard ta ruwaito shugaban kasa ya mika wa Hukumar tsaron ta SSS, sun hada da Farfesa Pat Etome, wani dan gwagwarmaya cikin al`amurran kasar nan da sanannen Babban Lauyan nan na Legas, shi ma dan gwagwarmaya musamman cikin kare hakkokin Bil Adama, wato Mista Femi Falana da tsohon Gwamnan Jihar Osun Mista Olugusoya Oyinlola da Mista Wale Edun Biolus da Babban Lauyan nan kuma Lauyan da ya kare Shugaba Buhari a zaben 2011, a lokacin da ya tsaya takara neman shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar CPC, takarar da bai yi nasara ba, a zaben 2011, wato Abubakar Malami.
A dai jerin sunayen da jaridar ta banguard ta ruwaito Hukumar tsaron ta SSS tana tantancewa, don nadawa Ministocin, akwai Janar Abdurrahaman Bello Danbazau mai ritaya, tsohon Babban Hafsan Askarawan kasa da akaita wa zargin a lokacin da ya ke kan karagar mulki a zamanin mulkin marigayi Shugaban kasa Alhaji Umar Musa `Yar`aduwa da abubuwa kasa ta tsaya cik a sanadiyar rashin lafiyar shugaba `Yar`aduwa ya ki amincewa a yi wa gwamnatin farar hula juyin mulki, soja su dawo da Misis Emiku Okoro.
Idan ka yi wa jerin sunayen duban tsaf za ka ga cewa sun kunshi `yan siyasa da `yan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, da gogaggun ma`aikata, ma`ana dai kusan dukkansu fitattu ne a harkokin rayuwar da suka sa gaba. Daga jerin sunayen da jaridar ta ruwaito kila ma da wadanda ake sa ran za su biyo baya zai iya tabbatar da cewa ba wasu waliyan mutane na daban ba ne, Shugaba Buharin zai nada Ministocinsa.
Wasu na da ra`ayin cewa kin nada Ministocin da Kwamishinoni a tararraya da jihohi da shugaban kasa da wadancan gwamnonin jihohi 21, ba su yi ba tamfar kokarin yin tsimi ne ga lalitar gwamnatocinsu idan aka yi la`akari da irin yadda shugaban kasa da akasarin gwamnonin jihohin suka samu gwamnatocinsu, na an yi wa tattalin arzikin kasar nan cin kaca, baya ga dimbin basussuka da ake bin gwamnatocinsu a ciki da wajen kasar nan.
Asibitocin sun kasance dakunan ba da shawara ga marassa lafiya, amma ba na warkarwa ba, saboda rashin magunguna da kwararrun ma`aikata da kayayyakin aiki, kamar yadda fannin ilmi ya ke fama da irin wadannan matsaloli na babu-babu da tabarbarewa, kama daga kan ilmin Firamare zuwa na Sakandare zuwa na manyan makarantu.
Wasu matsalolin da gwamnatocin wannan karon suka gada sun hada da rashin ayyukan yi musamman a tsankanin matasa da suka kammala karatunsu na manyan makarantu. Sai matsalolin kasa biyan albashi, tun daga kan gwamnatin tarayyar da wasu Hukumominta. Gwamnatocin jihohi 22, aka samu sun kasa biyan albashin ma`aikatunsu da ya kama daga wata daya zuwa watanni tara, al`amarin da ya kai fagen har wasu gwamnatocin suna yi wa ma`aikatansu barazanar za su rage musu albashi. Idan wasu na da ra`ayin Shugaba Buhari da wadancan gwamnonin jihohi 21, suna jan kafa ne akan yin tsimi a cikin lalitarsu. Ni kuma ina ganin jinkirin da suka yi zuwa wannan lokaci ya kara ba su cikakkiyar damar kara sanin a wane matsayi suka karbi gwamnati daga irin yadda suke ta kara samun bayanai daga manyan Sakatorin Ma`aikatu da suke hulda da su, tun da suka zo kan karagar mulki.
Babbar fatan da akasarin `yan kasa masu kuma kishin yadda za a gyara kasar daga irin tabarbarewar da kusan komai ya yi, bai wuce nada mutane nagari amintattu masu tsananin kishin kasar don zama Ministoci a tarayya da Kwamishinoni a jihohi. Ba wai sai wadanda suka bauta wa jam`iyyun siyasa ba, haka kuma zai iya samuwa ta hanyar tuntuba da bincike mai zurfi don zakulo wadanda suka dace da uwa uba yin adalci. Shugaban kasa da gwamnoni ko kusa kada su yi shayin sauke duk wani wanda suka fahimci dan gangan da ganganci a cikin tafiyarsu. Ta haka kawai kwallia za ta biya kudin sabulu.
Ana zaman jiran sunayen ministoci da kwamishinoni
A kowane lokaci `yan kasa suna zaman jiran jin jerin cikakkun sunayen irin mutanen da Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari zai mika wa Majalisar Dattawa…