Babban Alkalin Jihar Kaduna Mai Sharia Muhammad Lawal Bello ya ce ana yin fyade akalla 15 a kullum a jihar.
Mai Shari’a Muhammad Lawal Bello ya ce akasarin wadanda ake yi wa fyaden yara mata da maza ne ’yan watanni uku zuwa shakara 12.
“Matsalar fyade karuwa take yi a kasar nan har da jihar Kaduna domin muna samun fyade kusan 10 zuwa 15 a kullum.
“Kuma matsalar karuwa take yi inda wadanda abin ke shafa yara ne daga watanni uku zuwa shekaru 12.
“Yadda ake wa yara fyade abin damuwa ne matuka dole a tashi tsaye wajen magance matsalar kafin ya yi muni matuka,” inji shi.
Ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron da Kungiyar Lauyoyin Najeriya Reshen Jihar Kaduna a ranar Litinin.
A jawabinsa, Shugaban kungiyar a jihar Samson Audu kira ya yi ga gwamnati ta tashi tsaye wajen samar da kayan aiki na zamani domin magance kalubalen da sashen Shari’a ke fuskanta.