✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana tuhumar yayan Messi da yi wa wani barazana da bindiga

Rahotanni daga Ajantina sun ce Rundunar ’Yan sandan kasar tana tuhumar yayan Lionel Messi, mai suna Matias Messi da laifin yi wa wani barazana da…

Rahotanni daga Ajantina sun ce Rundunar ’Yan sandan kasar tana tuhumar yayan Lionel Messi, mai suna Matias Messi da laifin yi wa wani barazana da bindiga da hakan ya saba wa dokar kasar.

Rahoton ya ce wani mutum mai suna Jabier Ribera ne ya kai karar Matias Messi bayan sun yi taho-mu-gama a wani hadarin mota da ake ganin Matias din ne ya buga wa mutumin a lokacin da yake tukin ganganci.

Jim kadan bayan aukuwar hadarin sai Matias ya zaro bindiga daga cikin motarsa inda ya yi wa mutumin barazana amma da ya lura jama’a sun fara taruwa sai ya nemi guduwa.  A kan hanyarsa ce jami’an tsaro suka kama shi.

Rahoton ya ce an taba kama Matias da irin wannan laifi a shekarar 2015 da 2016 kuma a yayin bincike an same shi da miyagun kwayoyi da hodar Ibilis  da hakan ta sa jami’an za su tuhume shi.

dan shekara 35 Matias hatsabibin mutum ne da ake yawan samunsa da laifuffuka ba kamar kaninsa Lionel Messi da ya shahara a bangaren kwallon kafa a duniya ba.