✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana take hakkin dan Adam a Turkiyya

A sakamakon tsauraran matakan tsaro da hukumar bincike ta dauka na ba-gaira-ba-dalili a kan  magoya bayan babban Malamin nan, wato, Mallam Fettullah Gulen na Turkiyya,…

A sakamakon tsauraran matakan tsaro da hukumar bincike ta dauka na ba-gaira-ba-dalili a kan  magoya bayan babban Malamin nan, wato, Mallam Fettullah Gulen na Turkiyya, inda hukumar tsaro ta garkame mutane da dama ciki har da mata, inda suka yi amfani da cin zarafi, cin mutunci hade da duka, ga mutanen da ba su yi wani laifi ba.  
Rahotanni sun nuna cewar mutane arba’in da takwas (48) ne hukumar ta garkame a wurare daban-daban, wuraren da suka hada da, Bursa da Diyarbaki da Eskisehir da Istanbul da Kayseri da Manisa da kuma Tokat.
A yammacin ranar Littinin zuwa wayewar garin Talata nan ne kame-kamen da jami’an tsaron Turkiyya suka yi wa malamin da kuma magoya bayansa ya wakana.   Ana zargin mutanen ne da laifin samar da taimakon kudi ga wata kungiya da take adawa da gwamnatin Turkiyya da ake wa lakabi da (parallel structure) wanda hakan shaci-fadi  ne kawai ko kuma kirkirar shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ne, domin batanci ga babban Malami Fettullah Gulen.  Babu wata hujja da ta nuna malamin yana samarwa kungiyar da wani tallafi.
Kame-kamen da aka yi ya biyo bayan wata sanarwar zargin da kungiyar Hadin Kan kasashen Turawa (European Union) take yi wa gwamnatin Turkiya ne a bias sako-sakon da take yi wa ’yan ta’adda har suka samu gidin zama a kasar.
Kamen da aka yi a garin Manisa, ya gudana ne a karkashin babban Sufeton ’yan sanda tare da jami’ansa su kimanin 35 suka gudanar da kamen.
Kafar yada labarai ta Cihan da ke Turkiyya ta ce, likitoci da lawyoyi hade da ’yan kasuwa da Malaman makarantu kimanin (26) ashirin da shida ne aka taya keyarsu a yayin wannan kame a Manisa.  A wannan kame ciki har da wata babbar ma’aikaciyar Bankin ASYA wacce ta shahara a shekara 1996 wajen tallafa wa wata gungiya mai suna Hizmet wacce take kare hakkin dan Adam.
Jami’an tsaron sun sanya wa mutane 26 ankwa sannan suka aza keyarsu zuwa gidan kaso a cikin motocin da suka girke al’amarin da ya ja hankalin mutane har suka san abin da ke faruwa. Daga nan ne mutane suka rika tofa albarkacin bakinsu a kafofin yada da labarai da kuma a kafar sadarwar intanet.  Mutane sun yi Allah-tur da hakan.
Shugaban kotun Manisa wato Ali Arslan ya bayyana cewa an yi kamen ne ba bisa ka’ida ba.  Ya bayyana cewa hakan cin zarafin dan Adam ne.
Wasu da suka yi sharhi a kan al’amarin a shafukan abota wato (social media) sun kwatanta aukuwar hakan da irin wanda ya taba faruwa a Iraki, wato mutumin nan da hukumar tsaro ta Iraki ta cafke amma aka kai shi gidan kaso shi da matarsa ba tare da an sanya musu ankwa ba.
Hukumar tsaro ta nuna cewa ana sanya mai laifi ankwa ne kadai  idan ya nuna tirjiya ko kuma zai iya kawo barazana ga harkokin tsaro.
Arslan ya kara da cewa kamen da hukumr ta yi wa lanyoyi a bainar jama’a, tamkar tauye musu ’yanci ne. Ya ce wadanda aka garkamen mutane ne sanannu, kuma za a iya gayyatarsu don su bayar da kowane irin bayani a kowane lokaci ba tare an tozartasu a bainar jama’a ba.
 Arslan ya kara da cewa, sai da aka kai mutanen asibiti don a duba lafiyarsu kafin a zarce da su ofishin ’yan sanda don gudanar da bincike.  Yin haka kuma sam bai dace ba.
 Har yanzu ’yan sanda sun ce ana cigaba da neman mutane takwas da har yanzu ba a yi nasarar cafke wa ba.
Rahotani daga Cihan, sun sanar da cewar Jami’an tsaro sun auka dakin kwannan dalibai.   Jami’an tsaron sun ce sun yi amfani da takardun karatun daliban ne a amatsayin hujja ko shaida akan abin da take zargin Lauya Turgay kamar yadda shugaban da  jami’an tsaro suka auku musu gidaje ko ofis a yayin kamen ba tare da wani dalili ba, ya sanar a kafar sadarwarsa ta Twitter da misalign karfe 6 na safe a ranar Talata.
Shugaban ya ce wai  an gudanar da kamen ne a yunkurin da ’yan ta’adda suke na hambare  gwamnatin Turkiya ko kuma yi mata zagon kasa, al’amarin da ya musanta hakan.
Hukumar ’yan sanda ta watsa hotunan wasu mutane irin su Dailies Zaman da Bugun da Meydan da Taraf da kuma Aksiyon a kafofin yada labarai wanda take nema ruwa a jallo a matsayin wadanda suka tallafa wa ’yan ta’adda a Turkiyya.  Amma hakan ya samu suka daga wajen mafiy yawan mutane a kasar, inda suka nuna shakkunsu a kan wannan zargi
A lokuta da dama Shugaba Erdogan na  Turkiya da mukarrabansa suna sukar kungiyar Gulen ce wacce aka fi sani da Hizmet, wacce take karkashin jagorancin malamin  addinin musulunci wato Fettullah Gulen, wanda ake zargi da  ta’addanci, duk da rashin kwakkwarar hujja a game da wannan zargi.
Gulen mutum ne da aka san shi wajen sukar gwamnatin Turkiyya kuma yakan bayyanata  a matsayin gurbatacciya, wacce take nuna fifiko a bangaranci da kuma nuna kiyayya ga addini.
Shugaba Erdogan dai ya sha takura wa Gullen ta hanyar dana masa tarko, inda ta kai a watan Disambar shekarar 2013 ma ya ba da umarnin a kama iyalan  Gulen da wasu mukarraban gwamnati masu goya masa baya.
A watan Disambar shekarar 2014 ne Gwamnatin Turkiyya ta sanar da wata dokar yin kame ga duk mutumin da ake zargi da yunkurin tada hankalin gwamnati, kuma da alama gwamnatin ta yi haka ne don ta dana wa Gullen tarko don ta kama shi kuma sannan a muzanta shi. A da a kan duba girman laifi ne kafin a yi kame, amma yanzu hakan ya bada dama a yi kame ko da kuwa zargi ake yi.
Wannan wata dama ce ta cin zarafin al’umma ta hanyar karbe kayansu da wasu kadarori na mutanen da ake zargi da lafi ko kuma yunkurin hambare gwamnati.  Yin haka kuwa ba karamin tauye hakkin dan Adam ba ne, don haka muke kira da a gaggauta kawo karshen wannan al’amari a Turkiyya da ma a sassan duniya baki daya.
Sebagen Henry Noboh shi ne Shugaban Kamfanin CEOImpact Innobators Ltd da ke Buchanan Crescent inda aka saki Layin Aminu Kano Crescent, da ke Wuse 2, Abuja  Abuja Najeriya
Za a iya tuntubarsa a +234(0)81 6020 3993